Jam'iyyar APC Na Rasa Karfinta A Kudu Maso Kudu Yayin Da Ɗaruruwan Mambobinta Suka Koma PDP A Babban Jiha

Jam'iyyar APC Na Rasa Karfinta A Kudu Maso Kudu Yayin Da Ɗaruruwan Mambobinta Suka Koma PDP A Babban Jiha

  • Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na cigaba da fuskantar matsaloli a yankin kudu maso kudu
  • Daruruwan fitattun mambobinta sun fice daga jam'iyyar sun koma jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da ke mulki a jihar
  • Wannan sabon cigaban na kara nuna raunin APC a kudu maso kudu inda jihohin Ribas, Delta, Edo da Bayelsa duk ke karkashin PDP

Jihar Delta - Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta yi karo da matsala a jihar Delta biyo bayan ficewar wasu jiga-jiganta.

Kamar yadda Daily Independent ta rahoto, wasu manyan mambobin APC sun fita daga jam'iyyar a Delta ciki da Christian Onojacha (tsohon mai rike da mukami), Oddiri Igbru (tsohon dan takarar majalisa) da daruruwan mambobin jam'iyyar ta APC.

Abubakar Adamu
Zaben 2023: Jam'iyyar APC Na Karaya A Kudu Maso Kudu A Yayin Da Ta Rasa Mambobi Da Dama A Babban Jiha. Hoto: APC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Da Dumi: PDP Tayi Nasara Jam'iyyar APC Ba Tada Yan Takara a Kujerun Majalisar Rivers 16, Kotu ta Yanke hukunci

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda suka fice daga APCn sun koma jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ne.

Cif Val Arenyeka, mataimakin ciyaman din jam'iyya na mazabar Abraka 1 da Eku 9, ne ya tarbi sabbin wadanda suka shigo jam'iyyar.

Arenyeka, yayin tarbarsu, ya jinjinawa matakin da suka dauka na barin APC suka dawo PDP, yana mai basu tabbacin cewa za a tafi tare da su kamar kowanne mamba na jam'iyyar, rahoton Daily Independent.

Ya bukaci sabbin mambobin jam'iyyar su kasance cikin shiri a kowanne lokaci kuma su zama masu hikima wurin amfani da katin zabensu don fatattakar APC daga dukkan lunguna da sakunan jihar.

Odesenika Ejiro, shugaban mazabar Abraka PO Ward 1, da takwararsa Cif Friday Aghohhovia, wanda ke jagorantar mazabar Eku ta 9, ya ce wannan sabon cigaban alama ne da ke nuna cewa PDP ke da jihar Delta.

Hon. Felix Ejovwoke Erhimedafe, shugaban PDP na karamar hukumar Ethiope ta Gabas, ya ce PDP na da tabbas din samun kuri'u daga mutanensa a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata

Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Na PDP a Zamfara Ya Sauya Sheka Zuwa APC

A wani rahoton, dan takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Talata Marafa ta arewa karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Umar Yahaya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren labarai na APC a jihar, Malam Yusuf Idris ya saki a Gusau a ranar Juma’a, 11 ga watan Nuwamba, PM News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel