Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Na PDP a Zamfara Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Na PDP a Zamfara Ya Sauya Sheka Zuwa APC

  • Gabannin zaben 2023, jam'iyyar PDP ta rasa wani dan takararta na dan majalisa a jihar Zamfara
  • Umar Yahaya wanda ke neman kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Talata Marafa ta arewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Yahaya ya bayyana rikicin da yaki ci yaki cinyewa a babbar jam'iyyar adawar a matsayin dalilinsa na ficewa daga cikinta

Zamfara - Dan takarar kujerar dan majalisar jiha mai wakiltan mazabar Talata Marafa ta arewa karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Umar Yahaya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren labarai na APC a jihar, Malam Yusuf Idris ya saki a Gusau a ranar Juma’a, 11 ga watan Nuwamba, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku Ga Matasa: Ko Baku Da Kowa, PDP Zata Bude Muku Hanyoyin Samu

APC da PDP
Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Na PDP a Zamfara Yan Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: PM News
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta tuna cewa sauya shekar Yahaya na zuwa ne kwanaki biyar bayan dan takarar kujerar dan majalisar jihar na PDP a mazabar Gusau 2, Alhaji Ibrahim Mada ya sauya sheka zuwa APC.

Idris ya ce Yahaya ya samu tarba daga Gwamna Bello Matawalle da shugaban APC a jihar, Alhaji Tukur Danfulani, rahoton Peoples Gazatte.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idris ya ce:

“Dan takarar kujarer dan majalisar jiha na mazabar Talata Mafara ta Arewa a PDP, Umar Yahaya shima ya dawo daga rakiyar PDP a Zamfara.
“Yahaya ya ce ya yanke shawarar watsi da takararsa karkashin PDP don hada kai da APC saboda zargin rikici da ya dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsa a matakin kasa da na jiha.
“Ya bayyana cewa shugabancin PDP a jihar na mulkin kama karya sannan bata mutunta ra’ayin mambobinta.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata

Gwamna Matawalle ya jinjinawa Yahaya

Da yake martani, Matawalle ya yabama karfin gwiwar Yahaya na watsi da takararsa da kuma dawowa tafiyar APC a jihar.

Matawalle ya bayyana cewa APC jam’iyya ce mai maraba da duk mambobinta sannan ya bashi tabbacin dandana romon da sauran mambobin jam’iyyar ke sha.

Gwamnan ya bukace shi da ya wayarwa sauran mambobin tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP kai kan muhimmancin hada hannu wajen ciyar da Zamfara gaba.

Ya kara da cewa:

“Gwamnatina ta yi namijin kokari a bangaren tsaro, ababen more rayuwa, samar da aiki da kuma shugabanci mai nagarta.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel