Biyu Babu, Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata

Biyu Babu, Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata

  • Kotu ta kwace kujerar Sanata mai wakiltan mazabar Taraba ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya
  • Emmanuel Bwacha shine dan takaran kujerar gwamnan jihar Taraba karkashin jam'iyyar APC
  • Bwacha ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a watannin baya don ya nemi kujerar gwamna

Jalingo - Sanata Emmanuel Bwacha na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi biyu babu, ya rasa kujerarsa na Sanata a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba, 2022.

Haka Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba ta yanke.

Kotu ta fitittikeshi saboda sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa APC, rahoton Leadership.

Alkalin Kotuna, Simon Amobeda, ya umurci Sanatan ya gaggauta sauka daga kan kujerar.

Jam'iyyar PDP dai ta shigar da kara kotu inda ta bukaci a kori Bwacha daga kujerarsa saboda sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabeshi ya wakilci Taraba ta Kudu.

Kara karanta wannan

2023: Shettima ya caccaki Atiku da Obi, ya ce ba za su tsinanawa 'yan Najeriya komai ba

Bwacha
Biyu Babu, Kotu Ta Fitittiki Emmanuel Bwacha Daga Kujerar Sanata Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin APC a Taraba, Jam'iyyar APC Ba Ta Dan Takaran Gwamna a Zaben 2023

A watan Satumba kotun tarayya a Jalingo, ta soke zaben fidda gwanin dan takaran gwamnan jihar na jam'iyyar All Progressives Congress APC inda Emmanuel Bwacha yayi nasara.

Daya daga cikin yan takara zabe, David Sabo Kente, ne ya shigar da kara bisa zargin cewa murdiya aka yi

Kotun ta bayyana cewa ba'ayi zaben fidda gwani a Taraba ba, bisa hujjojin da aka gabatar gabanta.

Wannan Alkalin dai mai shari'a, Simon Amodeba, ne ya bada umurnin cewa a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 14.

Ya umurci Hukumar INEC ta soke sunan Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Taraba na jam'iyyar APC.

A Jihar Zamfara, abin kan PDP ya fada

Kara karanta wannan

Ta Kare Wa Atiku, Tsohon Shugaban PDP, Jiga-Jigai da Mambobi Sama da 40,000 Sun Koma APC a Arewa

A wani labarin kuwa, kotun tarayya a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara, ta soke dukkan zabukan fidda gwanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da akayi a jihar Zamfara.

A watan Yuni, wasu yan takara hudu suka shigar da kara kotu inda suka bukaci kotu tayi watsi da zaben.

Kotun ta bayyana cewa yanzu jam'iyyar PDP ba zata yi musharaka a zaben gwamna, yan majalisa da 2023 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel