Kotu Ta Ayyana Tsohon Minista a Matsayin Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC a Wata Jiha

Kotu Ta Ayyana Tsohon Minista a Matsayin Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC a Wata Jiha

  • Kotun Abuja ta ayyana tsohon ministan ma’adinai a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Abia
  • Mai shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ita ce ta zartar da hukuncin
  • Kotun ta ce Uche Ogah ne halastaccen dan takarar jam’iyyar mai mulki a jihar Abia ba Ikechi Emenike ba

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Uche Ogah, tsohon karamin ministan ma’adinai, a matsayin zababben dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Abia, jaridar TheCable ta rahoto.

A wani hukunci da ta yanke a ranar Juma’a, 11 ga watan Nuwamba, mai shari’a Binta Nyako ta soke takarar Ikechi Emenike wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sani a matsayin dan takara, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Mutum 8 Masu Jinin Najeriya Sun Lashe Kujerun Majalisa a Zaben Kasar Amurka

Uche Ogah
Da Duminsa: Kotu Ta Yi Fatali da Wanda Ya Ci Zabe, Ta Bayyana Halastaccen Dan Takarar Gwamnan APC a Wata Jiha Hoto: Uche Ogah
Asali: Facebook

Jam’iyyar APC reshen Abia ta gudanar da zaben fidda dan takarar gwamna a jihar wanda ya samar da Ogah da Emenike a matsayin yan takarar jam’iyyar.

A ranar 26 ga watan Mayu, APC ta ayyana Emenike a matsayin wanda ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda shari'ar ta fara daga babbar kotun Abia

Bayan haka, da take zartar da hukunci a wata kara da Chinedum Nwole da wasu biyu suka shigar, wata babbar kotun Abia ta ayyana cewa Emenike bai da hurumin takarar zabe saboda tun farko an dakatar da shi daga jam’iyyar.

Sai dai kuma, a wani hukuncin, alkalin kotun, O.A. Chijioke, ya zartar da hukunci inda Emenike yayi nasara.

Da yake zartar da hukunci a ranar 24 ga watan Yuni, kotun ta umurci APC da ta gabatarwa INEC da sunan Emenike sannan hukumar ta sanya sunansa a shafinta.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Hakazalika, kotun ta hana INEC karba ko wallafa sunan wani daban baya ga Emenike.

Uche Ogah ya daukaka kara bayan kotun Abia ta tabbatar da Emenike

Sai dai kuma, Uche Ogah wanda baya cikin shari’ar kuma bai shiga zaben fidda gwanin da ya samar da Emenike bay a tunkari kotun daukaka kara da nufin kalubalantar hukuncin.

Da yake adawa da lamarin, lauyan Emenike ya yi korafin cvewa kotun daukaka kara bata da hurumin sauraron karar tunda an shigar da ita ne bayan kwanaki 14 da aka ajiye na daukaka kara a lamuran zabe.

A ranar 20 ga watan Yuli, kotun daukaka karar ta riki batun kin amincewa da karar inda Emenike yayi nasara.

Amma Ogah ya sake shigar da wata karar a gaban babbar kotun tarayya ta Abuja.

Solomon Umoh, lauyan Ogah, ya fada ma kotun cewa jami’an INEC sun sanya idanu a zaben fidda gwanin da ya samar da wanda yake karewa sabanin wanda ya samar da Emenike.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Takarar Gwamna a Wata Jiha

Don haka, Ogah ya roki kotu da ta bayar da umurni ga APC na mika sunansa gaban INEC a matsayin zababben dan takarar gwamna a zaben Abia na 2023.

Hakazailka, Emenike ta hannun lauyansa, Lateef Fagbemi, ya roki kotun da ta riki zaben wanda yake karewa kan hujjar cewa shine ya bayyana daga zaben fidda gwanin da kwamitin NWC na APC ta gudanar.

Amma da take yanke hukunci, Nyako ta soke zaben da ya samar da Emenike a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Ta umurci APC da ta mika sunan Ogah ga hukumar INEC a matsayin zababben dan takarar gwamna na zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel