Mutum 8 Masu Jinin Najeriya Sun Lashe Kujerun Majalisa a Zaben Kasar Amurka

Mutum 8 Masu Jinin Najeriya Sun Lashe Kujerun Majalisa a Zaben Kasar Amurka

  • Wasu ‘Yan asalin Najeriya da ke ci-rani a Amurka sun shiga zaben ‘Yan Majalisa, sun kuma samu nasara
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da jawabin taya murna, ya kuma yi masu addu’ar yin dace a ofis
  • Gabe Okoye wanda a garin Enugwu-Aguleri a Anambra aka haife shi ya zama ‘dan majalisa a kasar Amurka

United States - Mutane takwas da ke da jinin Najeriya a jikinsu sun tashi da mukamai a zaben da aka gudanar a kasar Amurka a makon nan.

Premium Times tace Segun Adeyina, Gabe Okoye, Solomon Adesanya, Tish Naghise da kuma Phil Olaleye sun samu kujerun majalisa a jihar Georgia.

Baya ga mutane biyar da suka lashe kujerar majalisar tarayya a karon farko, akwai wadanda iyayensu ‘yan Najeriya ne da za su je majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Abin ya fara yawa: Ni da Masoyana Na Fuskantar Hadari Daga APC - Atiku Ya Koka

Carol Kazeem ta zama ‘yar majalisa mai wakiltar mazabar jihar Pennsylvania. Jaridar Vanguard tace Kazeem fitacciyar 'yar gwagwarmaya ce.

Sai Oye Owolewa da Esther Agbaje sun zarce a kan mukaman da suke kai. Owolewa zai cigaba da wakiltar mazabar Washington a majalisar wakilai.

Ita kuma Esther Agbaje ta doke ‘yan adaw a zaben kujerar majalisar dokoki. Agbaje za ta zarce a matsayin ‘yar majalisar jiha ta shiyyar Minnesota 59B.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amurka
'Yan Majalisar Amurka Hoto: www.amacad.org
Asali: UGC

Abike Dabiri-Erewa ta fitar da jawabi

Rahoton yace shugabar kwamitin da ke kula da ‘yan Najeriya da ke kasashen ketare watau NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta fitar da jawabi na musamman.

Abike Dabiri-Erewa ta taya wadanda suka lashe zaben murna, tace Najeriya tana alfahari da su.

A jawabinta, bayan ta yabi ‘yan siyasar, Dabiri-Erewa ta jinjinawa kwamitin NAPAC da ke taimakawa wajen tallata ‘Yan Najeriya a kasar ta Amurka.

Kara karanta wannan

Diyar Tsohon Shugaban Kasan Amurka Zata Auri ‘Dan Najeriya, Shagulgula Sun Kankama

...Buhari ya yi addu'a - Adesina

Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin Femi Adesina a ranar Laraba, yana mai murnar nasarar da ‘yan asalin kasarsa suka samu.

Kamar yadda Femi Adesina ya fada, shugaban Najeriya ya yi masu addu’ar samun nasara a wa’adinsu. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto dazu.

Tinubu da harkar kwayoyi?

An samu labari cewa a shekarun baya, an taba shari'a a kotu a kan akawun 10 da ke cikin bankunan ketare wanda Bola Tinubu da danginsa suka mallaka.

Kwamitin yakin neman zaben APC ya yi karin haske a kan lamarin, Festus Keyamo ya ce Dala $460, 000 da aka cire haraji ne, ba na harkar kwayoyi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel