Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Takarar Gwamna a Wata Jiha

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Takarar Gwamna a Wata Jiha

  • Jam’iyyar Labour Party ta hadu da sabon cikas a Enugu bayan wata babbar kotu da ke Abuja ta soke zaben gidda dan takararta na gwamna a jihar
  • Mai shari’a Nkonye Maha ya soke zaben fidda gwanin da ya samar da Chijioke Edeoga a matsayin dan takarar jam’iyyar ta LP
  • Da take zartar da hukunci a karar da Kyaftin Evarest Nnaji ya shigar, kotun ta yi umurnin sake sabon zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14 mai zuwa

Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta soke zaben Mista Chijioke Edeoga a matsayin dan takarar jam’iyyar Labour Party a zaben gwamnan jihar Enugu na 2023, jaridar Vanguard ta rahoto.

Da yake zartar da hukunci, Justis Nkonye Evelyn Maha, ya yi umurnin sake sabon zaben fidda gwani a cikin kwanaki 14, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa

Labour Party
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Takarar Gwamna a Wata Jiha Hoto: Vanguard

Justis Maha ya bayyana cewa jam’iyyar Labour Party ta gaza gabatar da shaidar sanar da zaben fidda gwanin na ranar 4 ga watan Agusta wanda da zai ba dukkanin yan takarar gwamna na jam’iyyar damar shiga zaben.

Kyaftin Evarest Nnaji ne ya shigar kara kan tsame shi da aka yi daga zaben fidda gwanin jam’iyyar na ranar 4 ga watan Agustan 2022 ba bisa ka’ida ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake korafin cewa jam’iyyar ta yi masa shigar sauri ta hanyar tsame shi a zaben fidda gwanin ba bisa doka ba, Nnaji, wanda aka fi sani da Odengene ya tunkari kotun Abuja don tabbatar da ko tsame shi da aka yi yana bisa doka ko akasin haka.

Nnaji ya maka jam’iyyar Labour Party da INEC a kotu, yana neman a ayyana shi a matsayin sahihin dan takarar gwamna na LP a jihar Enugu gabannin zaben 2023 ko a maimaita zaben.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP a Zamfara Ya Fusata, Ya Yi Kakkausan Martani Kan Hukuncin Kotu

Gobe Alhamis za a yi zaben kananan hukumomi a jihar Neja

A wani labarin kuma, mun ji cewa ana shirye-shiryen zabe a fdain kananan hukumomi 25 na jihar Neja a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba.

Gwamnatin jihar karkashin jagoranci Abubakar Sani Bello ta bayar da hutu a ranar Alhamis domin jama'a su fita su zabi yan takarar da suke so su wakilce su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng