'Ƙawancen' Buhari Da Tinubu Za Ta Wargaje A 2023, In Ji Atiku

'Ƙawancen' Buhari Da Tinubu Za Ta Wargaje A 2023, In Ji Atiku

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce kawancen da ke tsakanin Buhari da Atiku zai rushe a 2023
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin kaddamar da kwamitin kamfen dinsa reshen matasa
  • Atiku ya zaburar da matasan na kwamitin kamfen dinsa da su koma mazabunsu su isar da sakonsa na kawo sabuwar Najeriya a 2023

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana jam'iyyar APC mai mulki a matsayin 'kawance na biyan bukata' wanda zai rushe bayan shan kayensu a zaben shugaban kasa na 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kaddamar da reshen matasa na kwamitin kamfen dinsa a ranar Alhamis a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ban Rufe Kofar Sulhu Ba, Atiku Ya Bawa Wike Amsa

Atiku Abubakar N
2023: Ƙawancen Buhari Da Tinubu Za Ta Ruguje Bayan PDP Ta Kayar Da APC, Atiku. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku ya ce kasancewar PDP jam'iyya mafi tsufa a Najeriya, ta samu kwarewa da gogewa ta yadda za ta iya rike demokradiyyar kasar, The Punch ta rahoto.

Ya ce:

"Ka ga, maganar gaskiya, PDP ce kadai jam'iyyar siyasa a Najeriya. APC kawance ne tsakanin CPC da jam'iyyar Tinubu. Za mu kayar da su a zabe sannan za su mutu. Bana tunanin za su rayu bayan hakan."

Atiku ya zaburar da sabuwar kwamitin kamfen dinsa

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya bukaci sabuwar kwamitin kamfen din na matasa daga yankuna shida na kasar da su isar da sakonsa na fatan alheri zuwa dukkan lunguna da sakunan mazabunsu kuma su fahimtar da su manufofinsa na sake yi wa Najeriya fasali da ceto kasar.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP kuma gwamanan jihar Delta, Ifeanyo Okowa ya ce Najeriya da cikin halin damuwa a hannun APC kuma tana bukatar 'babban likita' wanda shine Atiku don ya farfado da ita daga sumar da ta yi.

Kara karanta wannan

Atiku Ga Matasa: Ko Baku Da Kowa, PDP Zata Bude Muku Hanyoyin Samu

Matsala Ga Atiku A Matsayin Dino Melaye Ya Yi Suɓutan Baki, Yace Yan Najeriya Su Zaɓi APC, FFK Ya Yi Martani

A wani rahoton, direktan sabuwar kafar watsa labarai na kwamitin kamfen din shugabancin kasa na Tinubu/Shettima, Femi Fani-Kayode, ya yi wa Dino Melaye, tsohon sanatan Kogi ta Yamma, izgili kan subutar bakin da ya yi a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Da ya ke jawabi wurin taron yakin neman zabe a Maiduguri a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, Melaye, kakakin kamfen din Atiku-Okowa, cikin kuskure, ya bukaci mutane su zabi APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel