Matsala Ga Atiku A Matsayin Dino Melaye Ya Yi Suɓutan Baki, Yace Yan Najeriya Su Zaɓi APC, FFK Ya Yi Martani

Matsala Ga Atiku A Matsayin Dino Melaye Ya Yi Suɓutan Baki, Yace Yan Najeriya Su Zaɓi APC, FFK Ya Yi Martani

  • Bisa ga dukkan alamu jigon jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode da na PDP, Dino Melaye ba su dena fada da juna ba
  • A wani abu a baya-bayan nan, tsohon ministan na sufurin jiragen sama ya yi wa Melaye izgili saboda cewa yan Najeriya su zabi APC a babban zaben da ke tafe
  • Domin kara tabbatar da lamarin, Fani-Kayode ya tafi shafinsa na Facebook ya kuma wallafa bidiyon Melaye, kakakin kamfen din Atiku

Facebook - Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma direktan sabuwar kafar watsa labarai na kwamitin kamfen din shugabancin kasa na Tinubu/Shettima, Cif Femi Fani-Kayode, ya yi wa Dino Melaye, tsohon sanatan Kogi ta Yamma, izgili kan subutar bakin da ya yi a Maiduguri, jihar Borno.

Da ya ke jawabi wurin taron yakin neman zabe a Maiduguri a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, Melaye, kakakin kamfen din Atiku-Okowa, cikin kuskure, ya bukaci mutane su zabi APC.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu NE dan takarar da ba zai wawuri kudin kasa ba idan ya ya gaji Buhari, inji jigon APC

Atiku in Borno
Matsala Ga Atiku A Matsayin Dino Melaye Ya Yi Suɓutan Baki, Yace Yan Najeriya Su Zaɓi APC, Femi Fani-Kayode Ya Yi Martani. Hoto: Vote and Stay
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Melaye ya yi magana ne yayin da ya ke zargin cewa an kaiwa tawagar kamfen din PDP hari a hanyarsu na zuwa jihar.

Fani Kayode ya yi martani

Da ya ke martani kan subutar bakin, Fani-Kayode ya ce kakakin na yakin neman zaben Atiku ya yi gaskiya.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Fani-Kayode ya rubuta:

"Tunda farko a yau, mai gadin bayan mota ya ce mutanen jihar Borno "APC za su zaba".
"A karon farko kuma ba mamaki karon karshe a rayuwarsa, ya fadi gaskiya!".

Dama dai, Fani-Kayode da Melaye sun kasance suna sukar juna a dandalin sada zumunta tun fara kamfen din takarar shugaban kasa a yayin da kowannensu ke yi wa mai gidansa aiki.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnan da ya muzanta Fulani ya kira su 'yan ta'adda ya nemi gafararsu

Fani-Kayode na yi wa Bola Tinubu aiki yayin da shi kuma Melaye na yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa aiki.

Rikicin PDP: "Sun Ci Amanar Jonathan, Yanzu Abin Ya Dawo Kansu", FFK Ya Ragargaji Atiku, Saraki Da Tambuwal

A yayin da ake cigaba da rikici tsakanin shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Mr Femi Fani Kayode, tsohon jigon jam'iyyar da yanzu ya koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, mai mulki ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin.

A cewar wani rubutu da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook, Mr Fani-Kayode ya zargi dan takarar shugaban kasar PDP, Atiku Abubakar, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, da Sanata Bukola Saraki da cin amanar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel