Atiku da Obi Ba Su da Wani Abin da Za Su Iya Yiwa ’Yan Najeriya, Inji Shettima

Atiku da Obi Ba Su da Wani Abin da Za Su Iya Yiwa ’Yan Najeriya, Inji Shettima

  • Abokin gamin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Kashim Shettima ya bayyana kwarin gwiwar lashe zaben 2023 mai zuwa
  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya ce ya ji dadin yadda aka hana wasu gwamnoni biyu takarar shugaban kasa a jam'iyyun APC da PDP
  • Wani jigon APC ya ce, Bola Ahmad Tinubu ne dan takarar shugaban kasan da ba zai wawuri kudin 'yan Najeriya ba idan ya gaji Buhari

Abuja - Abokin takarar Bola Ahmad Tinubu, Kashim Shettima ya bayyana cewa, babu wani abu guda daya da Atiku Abubakar da kuma Peter Obi za su iya yiwa 'yan Najeriya idan suka gaji Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Atiku Abubakar ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, shi kuwa Peter Obi, shi ke rike da tutar jam'iyyar Labour.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso ya ce ya ji dadin yadda APC da APC ba su ba wasu 'yan siyasa biyu tikitin gaje Buhari ba

Da yake magana a ranar Alhamis a Abuja a wani taron tallata manufofin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, Shettima ya bayyana abubuwan suka shiryawa 'yan Najeriya.

Shettima ya caccaki Atiku da Obi
Atiku da Obi Ba Su da Wani Abin da Za Su Iya Yiwa ’Yan Najeriya, Inji Shettima | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce, zaben 2023 mai zuwa zai zama babban tarihi ga Najeriya, kuma, Obi bai da wani abin da ya tsinana ko nunawa 'yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, abokin takararsa zai lallasa Atiku da Obi a zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu da Atiku ba za su tabuka komai ba, inji Kwankwaso

'Yan takara a Najeriya na ci gaba da musayar yawu a kasar nan yayin da ake tunkarar zaben 2023.

A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso cewa ya yi, sam Atiku da Tinubu ba za su tsinana komai a zaben 2023 mai zuwa ba, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

Ya kuma bayyana cewa, ya yi dadin yadda jam'iyyun PDP da APC ba su ba gwamna Wike da Umahi tikitin takarar shugaban kasa ba.

A cewar Kwankwaso, wadannan gwamnonin suna da kokari, kuma za su iya kawo masa tsaiko a tafiyarsa ta siyasa matukar ba a inuwa daya suke ba.

Tinubu ne dan takarar da ba zai wawuri kudin kasa ba, inji jigon APC

A wani labarin kuma, wani jigon APC ya ce, Tinubu ne dan takarar shugaban kasan da ba zai ci kudin 'yan Najeriya ba idan ya gaji Buhari.

Kakakin APC a jihar Zamfara, Yusuf Idris ne ya yaba da tsarin Tinubu, tare da bayyana irin alheran da dan takaran na shugaban kasa ya tanadarwa 'yan Najeriya.

Kadan daga ciki, ya ce Tinubu zai mai da hankali ga batun da ya shafi magance matsalolin tsaro da kuma habaka tattalin arzikin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel