Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

Ana nan tare: Gwamnan PDP Ya Karyata Rade-Radin Watsi da Tafiyar Atiku Abubakar

Gwamna Udom Emmanuel ba zai ajiye aikin da Atiku Abubakar ya ba shi na yakin neman zabe a PDP ba

Shugaban kwamitin neman takaran shugabancin kasar ya karyata rahoton cewa yana shirin murabus

Udom Emmanuel yace yana tare da takarar Atiku da Ifeanyi Okowa kuma Jam’iyyar PDP za ta dawo mulki

Akwa Ibom - Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, yace ba zai ajiye mukaminsa na shugaban kwamitin takarar Atiku Abubakar a PDP ba.

A ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba 2022, Vanguard ta rahoto Mai girma Udom Emmanuel yana musanya rade-radin barakar da wasu ke yadawa a PDP.

Gwamnan ya bayyana cewa shi cikakken mai biyayya ga jam’iyya ne, don haka babu abin da za isa ya yi watsi da takarar Atiku Abubakar/Dr. Ifeanyi Okowa.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Fadi Wanda Atiku Zai Mika Wa Mulki Bayan Gama Wa'adinsa

Babu abin da zai sa in canza gida - Udom

Udom Emmanuel yace babu matsin lambar da za a samu daga wani bangare da zai jawo ya yi fatali da yakin neman takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Channels TV ta rahoto Emmanuel yana cewa ba zai sauya-sheka ba, sai ya ga nasarar PDP.

Atiku
Atiku Abubakar a taro Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Jawabin Gwamna a wajen kamfe

“Har yanzu ni ne shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku-Okowa. Ba zan je ko ina ba. Sun ga za muyi nasara, shiyasa suke rade-radin murabus.
Kafin na shiga jawabi, bari in yi wa ‘Yan Najeriya bayani da farko. Na wayi gari da labarin karya cewa na yi murabus daga kwamitin neman zaben PDP.
Ba gaskiya ba ne. Mun doke su a baya, kuma za mu sake yin nasara. Mun shiga yakin neman zaben shugaban kasa ne saboda mu ci, ka da ku saurare su.

Kara karanta wannan

Atiku Yana Da Tambayoyi Da Zai Amsa Kan Alakarsa Da Yan Ta'adda, In Ji Fani-Kayode

Ina nan, ni ‘dan cikakken ‘dan jam’iyya ne mai yin biyayya. Ina nan a matsayin shugaban kwamitin neman takara. Ba zan je ko ina ba, za muyi nasara tare.”

- Udom Emmanuel

An rahoto cewa shugaban kwamitin zaben ya yi jawabi ne a wajen gabatar da Umo Eno wanda yake sa ran zai gaje shi a gidan gwamnatin jihar Akwa Ibom.

Atiku ya ki fito da kudi

A baya an samu labari cewa alamu na nuna tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya tsuke bakin aljihunsa a neman takaran da yake yi a zabe mai zuwa.

Gwamnonin PDP sun ki fito da kudi ana jiran Atiku Abubakar, idan aka cigaba da tafiya a haka, jam’iyyar za ta gamu da cikas wajen neman tunbuke APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel