Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Sabon Zaben Fidda Gwanin da Ta Canza a Kaduna

Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Sabon Zaben Fidda Gwanin da Ta Canza a Kaduna

  • Jam'iyyar PDP ta canza sabon zaɓen fidda ɗan takara a mazaɓar Sanatan Kaduna ta tsakiya bayan hukuncin Kotu
  • A zaben wanda ya gudanar ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, an samu sauyin ɗan takarar Sanatan karkashin inuwar PDP
  • Shugaban kwamitin shirya zaben ya ayyana Ibrahim Usman a matsayin wanda ya samu nasara da kuri'u 210

Kaduna - Ɗan majalisa a jihar Kaduna, Ibrahim Usman, ya lashe zaben fidda gwani na ɗan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Vanguard tace, Usman, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, ya tashi da ƙuri'u 210 daga cikin 223 da aka kaɗa wanda ya bashi damar lallasa abokan fafatawarsa 5.

Tambarin PDP.
Jam'uyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Sabon Zaben Fidda Gwanin da Ta Canza a Kaduna Hoto: channelstv
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Babbar Kotun tarayya dake zama a Kaduna ta rushe zaɓen fidda gwanin farko da PDP ta shirya a mazaɓar Sanatan Kaduna ta tsakiya ranar 24 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Goyon Baya, Jiga-Jigan PDP Sama da 300 Sun Koma Bayan Tinubu

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Muhammad Umar ta rushe zaɓen farkon ne saboda saba wa doka da aringizon kuri'u kana ta umarci PDP ta sake sabon zaɓe cikin kwanaki 14.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alƙalin ya yanke hukunci ne biyo bayan ƙarar da ɗaya ɗaga cikin 'yan takara, Ibrahim Usman ya kai gabansa, yana kalubalantar zaɓen farko wanda aka ayyana Lawal Adamu a matsayin wanda ya samu nasara.

Yadda sakamakon sabon zaben ya kasance

Bayan kammala sabon zaɓen wanda ya gudana ranar Litinin, shugaban kwamitin shirya zaɓen, Istifanus Mwansat, ya ayyana Ibrahim Usman a matsayin wanda ya zama zakara.

Yace Usman ya samu kuri'u 210 daga cikin kuri'un Deleget 223 da aka tantance su kaɗa kuri'unsu a tsakanin yan takara. 221 ne suka kaɗa kuri'unsu a zaɓen.

Lawal Adamu ya samu kuri'u biyar yayin da Farfesa Usman Muhammad Ya samu kuri'u biyu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dirama: Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata, Ya Takali Kakakin Atiku a Wurin Mahawarar Yan Takara

A wani labarin kuma Wani Babban Jigon APC da Wasu Shugabanni Sun Ayyana Goyom Baya Ga Ɗan Takarar PDP a 2023

Wani babban jigon APC da dumbin magoya bayansa sun ayyana goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kuros Riba a inuwar PDP.

Sam Bassey, tare da wasu shugabannin al'umma sun yanke wannan matasayar ne a wurin wani taro da suka gudanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel