Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata da Kalaman Kakakin Atiku a Wurin Muhawarar Yan Takara

Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata da Kalaman Kakakin Atiku a Wurin Muhawarar Yan Takara

  • Wani abu tamkar wasan kwaikwayo ya faru a wurin taron da aka shiryawa yan takarar shugaban kasa tsakanin Obi da Melaye
  • Lamarin dai wanda ya fara daga surutun da aka jiyo wani na yi, Peter Obi, ya nuna fushinsa kan dora laifin kan mutanensa
  • Kakakin kwamitin yakin neman zaɓen Atiku, Sanata Deno Melaye, ne ya fara takalar ɗan takarar jam'iyyar LP

Abuja - Da yammacin ranar Lahadi da ta gabata a wurin zaman da aka shirya wa masu neman shugaban ƙasa, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP, Peter Obi, ya nuna fushinsa na wasu daƙiƙu.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Obi ya nuna rashin jin daɗinsa ne kan wasu kalamai da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, Dino Melaye, ya yi a wurin.

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Yadda Wasu Matasa Suka Je Har Gida Suka Tube Wata Mata Tsirara

Peter Obi da Dino Melaye.
Bidiyon Yadda Peter Obi Ya Fusata da Kalaman Kakakin Atiku a Wurin Muhawarar Yan Takara Hoto: Peter Obi, Dino Melaye
Asali: Facebook

Ana tsaka da taron wanda Arise TV da haɗin guiwar Cibiyar raya demokuraɗiyya (CDD) ta shirya, sai surutu ya ɓarke kawai buɗar bakin Sanata Melaye yace magoya bayan Obi ne suka dami mutane da surutu.

Sai dai waɗannan kalaman basu yi wa Peter Obi daɗi ba domin fushi ya bayyana a fuskarsa kuma ya nemi ba'asin meyasa Melaye ya jefa laifin kan masoyansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kun ga abinda ke faruwa a nan, ba zan yarda da wannan cin kashin ba. Ya ɗora laifi kan mutanen Peter Obi. Mutumin ɗan ANPP amma har ya kira mutanen Peter Obi, to ya isheka haka, tun dazu kake takalata, meyasa ko da yaushe ni"

- Peter Obi ya maida martani ga Melaye a wurin taron.

Kalli Bidiyon abinda ya faru anan

Manyan 'yan takara biyu, Bola Ahmed Tinubu na APC da takwaransa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba su halarci wurin taron mahawarar da aka shirya musu ba.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Nemi Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Janye, Ya Mara Wa PDP Baya a 2023

Yayin da Atiku ya tura gwamna Okowa na jihar Delta ya wakilcesa, Tinubu bai tura kowa ba amma kwamitin kamfen APC yace ayyuka ne suka masa yawa shiyasa bai amsa gayyatar ba.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar Ya Sake Magana Kan Rikicinsa da Wike, Yace Sun Tsallake batun rikicin

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace ba zai yuwu a sauya shugabancin jam'iyyar PDP ba a yanzu.

Da yake tsokaci kan rikinsu da gwamnonin tsagin Wike, Atiku yace tuni ya daina damuwa kan batun ya matsa gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel