Wata Sabuwa: Jiga-Jigan APC da Masu Ruwa da Tsaki Sun Ayyana Goyon Baya Ga PDP

Wata Sabuwa: Jiga-Jigan APC da Masu Ruwa da Tsaki Sun Ayyana Goyon Baya Ga PDP

  • Wani babban jigon APC da dumbin magoya bayansa sun ayyana goyon bayan ɗan takarar gwamnan Kuros Riba a inuwar PDP
  • Sam Bassey, tare da wasu shugabannin al'umma sun yanke wannan matasayar ne a wurin wani taro da suka gudanar
  • Mista Bassey yace tsarin da jam'iyyar APC mai mulki ta ɗauka a jihar babu adalci ko kaɗan a ciki

Cross River - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Kuros Riba, Sam Bassey, da wasu shugabannin al'umma a yankin ƙaramar hukumar Biase, sun sha alwashin goyon bayan ɗan takarar gwamna a inuwar PDP, Sanday Onor.

Jaridar Premium Times tace sun ayyana haka ne a wurin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a garin Biase, kusa da Kalaba, babban birnin jihar.

Sanday Onor.
Wata Sabuwa: Jiga-Jigan APC da Masu Ruwa da Tsaki Sun Ayyana Goyon Baya Ga PDP Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Mista Bassey, ya bayyana cewa shi da masoyansa sun yanke marawa ɗan takarar gwamna na PDP baya duk da suna nan daram a cikin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Ciwan Kai Ga Atiku, Jam'iyyar APC Ta Ƙara Samun Gagarumin Goyon Baya Daga Wasu Jiga-Jigan PDP

Yace abinda suka shirya yi bai da alaƙa da cin amanar jam'iyyar ta ko wane fanni sai dai ma ya zama wani yunkuri na gyara, "rashin adalcin da aka yi wa mazaɓarsu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tsarin karɓa-karɓa da jam'iyyar APC a Kuros Riba ta runguma lokacin zaɓen fidda gwani rashin adalci ne ga mazaɓar Akamkpa/Biase ta tarayya, mahaifarmu baki ɗaya." inji shi.

Jigon, mamban ƙungiyar masoyan APC, yace lokaci ya yi da jam'iyyun siyasa zasu rika tabbatar da an yi adalci kuma ba'a zalunci kowa ba yayin kasafta ofisoshin siyasa.

Ya ƙara da cewa amfani da tsarin karɓa-karba ko makamantansu wurin hana ko zaluntar ƙananan yankuna ya saɓa wa tsarin yan uwantaka da juna.

Mista Bassey ya jaddada cewa kowace mazaɓar Sanata tana da mutane masu kwarewa da zasu mulki jihar, sannan ya nuna damuwarsa cewa ɗan takarar Sanata da gwamna duk sun fito nr ɗaga Efik, yanki ɗaya.

Kara karanta wannan

Karshen Zamani: Yadda Wasu Matasa Suka Je Har Gida Suka Tube Wata Mata Tsirara

Ba zan goyi bayan Atiku ba - Ortom

A wani labarin kuma Gwamnan Benuwai Ya Ɗau Zafi a PDP, Yace Gara Ya Mutu da ya mara wa Atiku Abubakar baya a 2023

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace ba zai mara wa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar baya ba a 2023

Gwamnan, wanda ya fito daga arewacin Najeriya yace ya gwammaci ya mutu da ya goyi bayan Bafullatani ya zama shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel