Abubuwa Sun Sukurkucewa PDP, Gwamnan Arewa Yana Barazanar Yin Watsi da Atiku

Abubuwa Sun Sukurkucewa PDP, Gwamnan Arewa Yana Barazanar Yin Watsi da Atiku

  • Alamu na nuna Gwamna Bala Mohammed ya yi fushi da yadda abubuwa suke tafiya a Jam’iyyar PDP
  • Wannan ya jawo Jam’iyyar PDP ta aika wata tawaga ta musamman da nufin a iya shawo kan Gwamnan
  • Bala Mohammed yana zargin cewa Atiku Abubakar bai goyon bayan tazarcen da yak enema a zaben 2023

Bauchi - An shiga wani hali a jam’iyyar PDP a dalilin barazanar da Gwamna Bala Mohammed yake yi na yin watsi da batun yi wa Atiku Abubakar kamfe.

The Nation tace Mai girma Bala Mohammed ya yi fushi da PDP ne bayan ya samu bayanai da ke zargin Alhaji Atiku Abubakar bai goyon bayan tazarcensa.

Gwamnan na jihar Bauchi ya koka da cewa an ki ba shi dama ya jagoranci yakin neman zaben Atiku Abubakar a yankin Arewa maso gabas inda ya fito.

Kara karanta wannan

Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Duk da shi ne mataimakin shugaban kwamitin yakin zaben PDP a bangaren Arewa maso gabas, Gwamnan mai neman tazarce bai maida hankali a kamfe ba.

Atiku ya yi watsi da Bala?

Sanata Mohammed ya nuna a duk cikin wadanda suka nemi tikitin PDP, shi kadai ne wanda Atiku bai kawowa ziyara domin a sasanta, a dinke baraka ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace tsohon Ministan na birnin tarayya ya janye jikinsa daga yakin neman zaben 2023.

Atiku Abubakar
Bala Mohammed da Atiku Abubakar Hoto: www.withinnigeria.com
Asali: UGC

PDP ta aika tawaga zuwa Bauchi

A dalilin haka ne jaridar The Cable tace Shugaban PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu ya jagoranci tawaga zuwa wajen Gwamnan a ranar Asabar da ta gabata.

Tawagar Iyorchia Ayu ta kunshi Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon Jigawa, Sule Lamido domin su shawo kan rikicin cikin gidan jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Jagororin na jam’iyyar sun yi taron ne ba tare da sanin abin da aka tattauna a bayan labule ba.

Da yake jawabi, Ayu ya shaida cewa sun zo garin Bauchi ne la’akari da tirka-tirkar da ake fama da ita a jihar, don haka suka nemi Gwamna ya bada shawara.

Shugaban PDP na kasa ya yabi Bala Mohammed, yace yana cikin wadanda suka taimakawa jam’iyya. Gwamnan yace za ayi magana ne a kan yakin 2023.

Ikpeazu ba zai yi APC ba

A baya kun samu rahoto cewa ana yada jita-jita cewa Gwamnan Abia yana cikin Gwamnonin PDP za su taimakawa Bola Tinubu domin ya ci zabe a 2023.

Wani ‘dan kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Abia, John Okiyi Kalu yace Okezie Ikpeazu bai goyon bayan Jam’iyyar APC da 'dan takaran na ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel