Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Ana Zargin Gwamnan PDP da Ya Raba Jiha da Atiku Zai Yi wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

  • Wani ‘dan kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar yace Okezie Ikpeazu bai goyon bayan Jam’iyyar APC
  • Ana yada jita-jita cewa Gwamnan Abia yana cikin wadanda za su taimakawa Bola Tinubu domin ya ci zabe
  • John Okiyi Kalu wanda yayi aiki da Gwamnan, ya tabbatar da cewa APC da Tinubu ba su a cikin lissafin

Abia - Wani daga cikin ‘yan majalisar yakin neman zaben PDP a jihar Abia, John Okiyi Kalu ya yi watsi da batun sauya-shekar Gwamna Okezie Ikpeazu.

Vanguard tace rade-radi na yawo cewa Mai girma Dr. Okezie Ikpeazu zai iya barin jam’iyyar PDP, ko kuma ya taimakawa ‘dan takaran APC, Bola Tinubu.

A wani jawabi da Cif John Okiyi Kalu ya fitar a karshen makon da ya wuce, ya tabbatar da cewa Gwamnan Abia ba zai taba goyo bayan APC a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Tinubu, Atiku Sun Gagara Halartar Taron ‘Yan Takara, Kwankwaso, Obi Sun Yi Kasuwa

Kamar yadda Sun tace John Kalu ya shaidawa 'yan jarida, masu tunanin Okezie Ikpeazu zai taimakawa APC mai mulki a zaben badi, su na bata lokacinsu.

‘Dan kwamitin yakin neman zaben yake cewa rikicin Gwamnan mai barin gadon a 2023 da PDP shi ne yana so a rika damawa da kowane yanki a siyasa.

Maganar John Okiyi Kalu

"Idan ka san Gwamna Okezie Ikpeazu, ba za ka ambaci sunansa tare da zaben Bola Tinubu na APC, ko ya taimakawa nasararsa ba, haka ba zai taba faruwa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna da Atiku
Gwamna Okezie Ikpeazu da Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Jita-jitar cewa Okezie Ikpeazu yana cikin wasu Gwamnonin jihohi hudu da za su marawa Bola Tinubu baya, kanzon-kurege ne na mai rubutu kurum.
Ya bayyana matsayarsa a fili da boye yayin da ya tattauna da jagororin PDP a matakin jiha da na tarayya, har yanzu yana nan a jam’iyyar adawa ta PDP.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigo Ya Gargadi Jam’iyya, Yace ‘Dan Takaran Kano Yana Tare da Atiku

Shi Mai martaba Okezie Ikpeazu, PhD yana so shugabannin jam’iyyarsa, su tafi da kowane bangare a kasar nan, hakan bai nufin barin PDP ko bin APC.

- John Okiyi Kalu

Tinubu bai cikin lissafin Okezie Ikpeazu

An rahoto Kalu yace a matsayinsa na wanda ya yi aiki da Ikpeazu, zai iya cewa duk rikicin da ake yi a PDP, Tinubu da APC ba su cikin zabinsa na ukun farko.

‘Dan siyasar bai bayyana su wanene Gwamnan zai iya goyon baya idan ba samu jituwa da Atiku Abubakar ba, amma yace babu ruwan Ikpeazu da Bola Tinubu.

APC ra rasa mutane a Sokoto

An ji labari cewa Shugaban APC, Isah Sadik Achida yace wasu ‘yanuwan Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal sun dawo tafiyarsu bayan tsallokowa daga PDP.

Alhaji Habibu Waziri Tambuwal yana cikin wadanda suka rabu da Mai girma Gwamnan Sokoto kuma Shugaban yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Asali: Legit.ng

Online view pixel