APC da Tinubu Na Shirin Ba Atiku Mamaki a Adamawa, Za a Tika Shi da Kasa a Mahaifa

APC da Tinubu Na Shirin Ba Atiku Mamaki a Adamawa, Za a Tika Shi da Kasa a Mahaifa

  • Shugaban matasan jam’iyyar APC na fadin Najeriya ya kai ziyara zuwa mahaifar Atiku Abubakar
  • Dayo Israel ya karbi wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da suka tsallako zuwa shekar APC a shirin 2023
  • Israel yace wannan ya nuna Bola Tinubu zai yi nasara a Adamawa, kuma APC za ta ci zaben Gwamna

Adamawa - Shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel, yana sa ran za su lallasa PDP a jihar Adamawa a zaben Najeriya da za ayi a 2023.

Duk da Adamawa ce mahaifar Atiku Abubakar, Daily Trust ta rahoto Dayo Israel yana cewa jam’iyyar APC da ‘dan takararta ne za su yi galaba a jihar.

Dayo Israel ya bayyana wannan a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Yola, bayan ya karbi daruruwan magoya bayan PDP da suka dawo jam’iyyarsu.

Shugaban matasan na APC yace sauya-shekar ‘ya ‘yan PDP a jihar ya nuna alamun nasarar da jam’iyyarsa za ta samu a zabukan da za a shirya a badi.

APC za ta ci zaben Gwamna a Adamawa

A cewarsa, baya ga kuri’un da jam’iyyar APC za ta tashi da su a zaben shugaban kasa, za kuma suyi nasarar karbe kujerar gwamna daga hannun PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta na sane PDP ce take rike da mulki a jihar Adamawa tun 2019, Ahmadu Fintitri ya tika Gwamna Jibrila Bindow na APC da kasa.

Atiku
Atiku a Adamawa Hoto: solacebase.com
Asali: UGC

Wannan karo APC ta tsaida Sanata Aisha Binani, sai dai takararta na fuskantar kalubale a kotu. Tun yanzu Israel ya hangowa APC gagarumar nasara.

Matashin yake cewa mutanen jihar Arewa maso gabashin kasar su na cikin wadanda za su bada gudumuwa ga inubu wajen doke Wazirin Adamawa.

Da su Adamawa Tinubu zai samu mulki

“Jihar Adamawa za ta taka babbar rawar gani wajen zaman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.
Za a ce farin jininsa ya girmama, nasararsa tayi karfi, har mutanen abokin adawarsa sun fi ganin cancantar darewarsa mulki.
A dalilinku, da kokarin da za muyi, da shirye-shiryen da Asiwaju Bola Tinubu yake yi wa mutanen Adamawa, zai ci jihar nan a badi.

- Dayo Israel

Ayu zai hallaka PDP - CUPP

Dazu an ji labari cewa Kakakin Kungiyar hadakar jam’iyyun siyasa watau CUPP yace Dr. Iyorchia Ayu ya kama hanyar rugurguza Jam’iyyarsa ta PDP.

Ikenga Imo Ugochinyere ya gargadi Ayu ya yi murabus tun wuri, ya zarge shi da neman ganin bayan abokan rigimarsa saboda sabanin cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel