2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu

  • Wasu yan takarar guda hudu na jam'iyyar NNPP sun yi watsi da Kwankwaso sun mara wa Bola Tinubu baya a Osun
  • Clement Bamigbola, wanda ya yi magana a madadin yan takarar hudu ya ce sun janye goyon bayansu ga Kwankwaso ne saboda rashin gamsuwa da shugabancin jam'iyyar a matakin kasa
  • Bamigbola ya ce sun yi shawara tare da samun hadin kai daga magoya bayansu kafin su dauki matakin suna mai cewa Tinubu zai lasa wa kowa romon demokradiyya

Osun - Mutum hudu cikin wadanda za su yi takara a zaben 2023 karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a Jihar Osun, a ranar Laraba sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Sanata Bola Tinubu.

Yan takarar, Clement Bamigbola, dan takarar sanata na Osun Central; Bolaji Akinyode, dan takarar sanata na Osun West; Olalekan Fabayo da Oluwaseyi Ajayi, yan takarar majalisar tarayya na Boluwaduro/Ifedayo/Ila, da Ijesa South kamar yadda aka jero.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigai masu goyon bayan Wike sun yi hannun riga da kwamitin kamfen PDP

Kwankwaso da Tinubu
2023: Manyan Yan Takarar NNPP A Osun Sun Juya Wa Kwankwaso Baya, Sun Rungumi Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Kwankwaso
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa yan takarar na NNPP suka juya wa Kwankwaso baya

Yan takarar hudu sun ce sun janye goyon bayansu ga Kwankwaso suka koma goyon bayan Tinubu saboda rufa-rufa da ake yi wurin gudanar da harkokin jam'iyyar a matakin kasa, The Punch ta rahoto.

Da ya ke magana da yan jarida a Osogbo a madadin sauran yan takarar, Bamigbola ya ce:

"Duba da abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar mu kuma bayan tuntubar da samun amincewar magoya bayan mu, muna son sanar da goyon bayan mu ga dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu.
"Hakan ya biyo bayan rashin gamsuwa da muka yi da shugabannin jam'iyyar a matakin kasa tare da gazawar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar na yin aiki da adalci, doka da tsarin demokradiyya wurin gudanar da harkoki a jam'iyyar mu."

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Tinubu zai lasa wa kowa romon demokradiyya - Bamigbola

Ya kara da cewa yana tabbatar wa magoya bayansa cewa za a samu jagoranci mai kyau kuma kowa zai lashi romon demokradiyya karkashin shugabancin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel