2023: Ortom da Dattawan Benue Sun Janye Daga Goyon Bayan Dan Takarar PDP Atiku

2023: Ortom da Dattawan Benue Sun Janye Daga Goyon Bayan Dan Takarar PDP Atiku

  • Gwamnan jihar Benue ya bayyana yin waje da tafiyar Atiku Abubakar saboda wasu maganganu da suka fito
  • Samuel Ortom da gwamna Wike na Ribas sun sha nuna adawarsu ga yadda tafiyar takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ke tafiya
  • Har yanzu akwai sauran kura a jam'iyyar PDP yayin da babban zaben 2023 ke kara gabatowa nan ba da jimawa ba

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom a ranar Talata ya bayyana janyewarsa daga goyon bayan dan takarar shugaban kasan jam'iyyarsu ta PDP, Atiku Abubakar.

Ortom ya zargi Atiku da rashin martaba shi a matsayinsa na gwamna kuma yana tafiya nesa da manufofin jihar Benue da al'ummar jihar, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan martani na Ortom ya zo ne jim kadan bayan da wata tawaga ta dattawan Benue ta Minda Leaders of Thoughts ta bayyana nesanta kanta da takarar Atiku bisa zargisa da yin magana mai tada kiyayya.

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan PDP mai ba Atiku ciwon kai ya zabo tsohon jigon APC ya zama kwamishinansa

Gwamna Samuel Ortom ya barranta daga tafiyar Atiku
2023: Ortom da Dattawan Benue Sun Janye Daga Goyon Bayan Dan Takarar PDP Atiku | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Alamu na nuna cewa, Ortom ya kullaci Atiku ne tun bayan martanina ga wasu kashe-kashe da suka faru a jihar Benue da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku dan aikin Miyetti Allah ne

Hakazalika, ya zargi Atiku da yiwa kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, wacce yace kungiyace mai mallakar makamai.

A cewar Ortom:

"Ba daidai bane dan takarar shugaban kasa wanda ke neman ya mulki jama'a ya fadi irin wannan abin ba.
"Babban kuskure ne. Kuma ma gani nayi bai ma mutunta ni ba ya ganni a matsayin gwamna na jiha ta."

Bana cikin 'yan kamfen din Atiku - damuwar gwamna Ortom

Hakazalika, Ortom ya zargi Atiku da mai dashi saniyar ware a lokacin da yake zaban tawagar gangamin kamfen dinsa na takarar shugaban kasa.

A cewarsa:

"Bana cikin tawagar kamfen dinsa. Mutanen da suka nada a can, ba su da izini na. Don haka ni ina nan ni kadai. Amma ina jira; lokacin da zabe yazo, za mu yi zaben ne a yadda yazo."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Ortom dai daya ne daga cikin wadanda ke kalubalantar shugabancin jam'iyyar PDP tun bayan kammala zaben fidda gwani da kuma nada Okowa a matsayin abokin takarar Atiku.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ne ummul-khaba'isin duk wata fitina a jam'iyyar PDP, kamar yadda Channels Tv ta tattaro.

Tsohon Jigon APC a Ribas Chris Finebone Ya Fito a Jerin Sabbin Kwamishinonin Wike

A wani labarin, Mr. Chris Finebone, tsohon kakakin APC a jihar Ribas ya fito a jerin sunaye 18 na sabbin kwamishinonin da gwamnan PDP Wike ya mika majalisar dokokin jiharsa domin tantancewa.

Finebone, wanda dan a mutun minista kuma tsohon gwamna Rotimi Amaechi na APC ne ya kasance mai tsananin suka ga tafiyar gwamnatin Nyesom Wike na PDP.

Sai dai, an samu rahotannin dake bayyana cewa, Finebone ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a baya, kamar yadda PM News Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.