Tsohon Jigon APC a Ribas Chris Finebone Ya Fito a Jerin Sabbin Kwamishinonin Wike

Tsohon Jigon APC a Ribas Chris Finebone Ya Fito a Jerin Sabbin Kwamishinonin Wike

 • Siyasar jihar Ribas na ci gaba da zama wata kama yayin da gwamnan PDP ke kokarin harmutsa lamuran jam'iyyar da sauran jam'iyyu
 • An bayyana wani tsohon jigon APC da ya sauya sheka a jerin sunayen wadanda gwamnan ya zaba su zama kwamishinoninsa
 • Ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamna Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar

Jihar Ribas - Mr. Chris Finebone, tsohon kakakin APC a jihar Ribas ya fito a jerin sunaye 18 na sabbin kwamishinonin da gwamnan PDP Wike ya mika majalisar dokokin jiharsa domin tantancewa.

Finebone, wanda dan a mutun minista kuma tsohon gwamna Rotimi Amaechi na APC ne ya kasance mai tsananin suka ga tafiyar gwamnatin Nyesom Wike na PDP.

Sai dai, an samu rahotannin dake bayyana cewa, Finebone ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a baya, kamar yadda PM News Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kalaman Wani Gwamnan PDP Kan Kamfen Atiku Ya Tada Kura, An Nemi Ya Yi Murabus

Tsohon jigon APC ya zama kwamishina a jihar Ribas
Tsohon jigon APC a Ribas Chris Finebone ya fito a jerin sabbin kwamishinonin Wike | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

An taba naqalto shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutane basu fahimci gwamna Wike bane. Idan ka kusance shi, za ka fahimci mutum ne mai babbar zuciya."

Ko ma dai yaya ne, yanzu yana daga cikin wadanda gwamnan ya zaba za su zama kwamishinoni, kamar yadda ya fito a wata takarda daga majalisar dokokin jihar Ribas, Stanford Oba.

Sanarwar ta ce:

"Majalisar dokokin jihar Ribas na gayyatar wadannan da aka zaba su bayyana a gabanta a ranar Talata 25 ga watan Oktoba 2022 da misalin karfe 9 na safe domin tantance su ga kujerun kwamishina."

Jerin wadanda aka zaba su zama kwamishinoni

Ga dai jerin sunayen da gwamnan ya bayar kamar yadda jaridar Punch ta tattaro.

 1. Prof. Princewill Chike
 2. Hon. Jacobson Nbina
 3. Mr. Ndubuisi Okere
 4. Barr. Mrs Inime Aguma
 5. Engr. Charles Amadi
 6. Mrs. Tonye Oniyinde Briggs
 7. Mr. Ben Daminabo
 8. Chris Finebone
 9. Engr. Austin Ben Chioma
 10. Mr Uchechukwu Nwafor
 11. Dr. Fred Barivule Kpakol
 12. Barr. Emenike Oke
 13. Mr. Prince Ohia
 14. Prof. Kaniye Ebeku
 15. Mr. Ezekiel Agri
 16. Mrs. Ukiel Oyaghiri
 17. Hon. Damiete Herbert Horsfall
 18. Hon Emeka Onowu

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna da Wasu Sun Koma PDP

Hakazalika, sanarwar ta nemi su kawo kwafin takardun shaidar karatunsu guda 35 da kuma takardun sahhalewar haraji ga ofishin majalisar.

Dan Takarar APC Tinubu Ya Gana da Malaman Addinin Kirista a Jihar Kano, Ya Yi Musu Jawabi

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya gana da wasu manyan malaman addinin kirista a jihar Kano ta Arewa maso Yammacin Najeriya.

A wani bidiyon da aka yada na Tinubu, an bayyana lokacin da yake yi musu jawabi game da hadin kai da kuma zaman lafiya da kamanceceniya tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya.

Tinubu ya bayyana cewa, hanya daya Musulmai da Kiristoci ke bi wajen neman gafara, kamar dai yadda yazo a Al-Qur'ani a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel