Hadimin Tambuwal, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Dandazon Mambobi Sun Koma APC

Hadimin Tambuwal, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Dandazon Mambobi Sun Koma APC

  • Makonni uku bayan fara kamfen 2023, jam'iyyar APC ta kara samun gagarumin goyon baya a jihar Sakkwato
  • Hadimin gwamna Aminu Tambuwal da mataimakin shugaban PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da magoya bayansu
  • Haka zalika daruruwan mambobin PDP a garin Gadanme, karamar hukumar Silame ta jihar sun rungumi tsintsiya

Sokoto - Hadimin gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato na musamman, (SA), Alhaji Garba Tozai, da mataimakin shugaban PDP a ƙaramar hukumar Isa, Garba Araga, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa jigan-jigan biyu sun tattara kayansu zuwa APC ne tare da ɗumbin magoya bayansu dake dukkan sassan jihar Sakkwato.

Sauya sheka a Sakkwato.
Hadimin Tambuwal, Mataimakin Shugaban PDP da Wasu Dandazon Mambobi Sun Koma APC Hoto: vanguard
Asali: UGC

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Sanata Aliyu Wamakko, Bashar Abubakar ya fitar ranar Asabar a birnin Sakkwato.

Kara karanta wannan

2023: Gangamin Taron Kamfen PDP a Edo Ya Sake Fito da Rikicin Jam'iyyar, Atiku Ya Shiga Matsala

Abubakar ya haƙaito tsohon mataimakin shugaban PDP, wanda ya yi jawabi a madadin masu sauya shekar, na cewa sun yanke wannan matakin ne duba da ƙarfin masu ruwa da tsakin APC a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna da kwarin guiwar cewa bisa la'akari da cigaban da ake samu a shiyyarmu, PDP ta zama tarihi. Yau gamu a APC muna da jagora Kanal mai ritaya Garba Moyo, tsohon kwamishina a gwamnati mai ci ta PDP."
"Bugu da kari, tare da Alhaji Ibrahim Lamido a matsayin takarar Sanata a shiyyar mu babu tantama za'a share mana hawayenmu."

- Garba Araga.

Mista Araga ya kara da yabon Sanata Wamakko, jagoran APC a jihar Sakkwato tare da alkawarin zasu ba da haɗin kai da aiki a tare da juna don tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaben 2023.

Daruruwan mambobin PDP sun Koma APC

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayan shafe kwanaki a Faransa, dan takarar PDP Atiku ya dawo Najeriya

A wani cigaba makamancin wannan, jam'iyyar APC ta karbi dandazon masu sauya sheka daga jam'iyyar PDP a garin Gadambe dake ƙaramar hukumar Silame.

Da suke karɓan tuban masu sauya shekar, shugaban kwamitin rikon kwarya a yankin, Alhaji Dalhatu Dantama, da wani jigon APC, Alhaji Abubakar Rana, sun tabbatar musu da ba za'a nuna musu banbanci ba.

Wani Jigon APC a Sifawa, karamar hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato, Idris Shehu, ya tabbatar da lamarin ga wakilin Legit.ng Hausa, yace hadimin gwamnan ya yi murabus sannan ya koma APC.

A zantawarsa da wakilinmu, Shehu yace jam'iyyarsa APC ta shirya tsaf domin kwace mulki daga hannun PDP a jihar idan aka yi la'akari da faruwar irin haka kuma yace wannan somin taɓi ne.

A cewarsa, "Kashi 80 cikin 100 na mutanen Sakkwato bamu jin daɗin mulkin PDP tun farko, idan ka duba gwamna ya yi nasara da kuri'u 342 a zaben 2019, alamu sun nuna mutane ba su jin daɗi."

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

A wani labarin kuma Jigon PDP Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi a 2023

Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a kasar nan, Dr Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi ne zabinsa a babban zaben 2023.

Orji, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Abiya a inuwar PDP, yace Atiku abokinsa ne amma Obi ya fi shi cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel