Zaben 2023: Najeriya Za Ta Wargaje Idan Tinubu Ya Yi Nasara, Gwamna Obaseki
- Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce idan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya ci zaben 2023, Najeriya za ta rabu
- Obaseki ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 21 ga watan Oktoba a Edo wurin rantsar da mambobin kwamitin kamfen na jihar Edo
- Gwamnan na Edo ya ce babu wata gwamnati ta ta taba yi wa Najeriya ila kamar ta APC mai ci yanzu don haka bai kamata a bari ta sake komawa kan mulki ba
Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ce Najeriya za ta rabu idan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ci zaben shugaban kasa na 2023, rahoton Daily Trust.
Bola Tinubu, dan takarar jam'iyyar mai mulki a kasa zai fafata da Atiku Abubakar na PDP da wasu yan takarar a zaben da za a yi a watan Fabrairun 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da ya ke jawabi wurin rantsar da ya kwamitin kamfen a ranar Litinin, Obaseki ya ce PDP za ta yi iya kokarinta don ganin ta ci zaben shugaban kasa da mafi yawancin kujerun majalisar kasa.
Babu wanda ya taba irin barnar da gwamnatin APC mai ci yanzu ta yi wa Najeriya - Obaseki
Ya ce:
"Na yi imanin wannan nasarar za ta zo mana da sauki idan muka yi kamfen din mu yadda ya kamata. Ya kamata a duba kwakwalwar mu a matsayin yan Najeriya idan muka yi tunanin zaben gwamnati kamar APC. Allah ya kyauta idan APC ta hau mulki; kasar nan za ta rabe; kasar nan za ta gaza. Ta ma gaza.
"Babu wanda ya taba yin irin barnar da gwamnatin APC mai ci yanzu ta yi wa kasar nan. Ban san yadda za mu farfado ba. Mun lalata turban kasarnan. Da ikon Allah, dan takarar mu zai yi nasara. Za mu dawo da Najeriya; za mu sanar da kasar. Za mu rage banbancin kuma za mu fara gina kasarmu ta hanyar da Ubangiji ya ce."
2023: Atiku Ya Maida Zazzafan Martani Ga Bola Tinubu Kan Kalaman Dubai
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, yace bai kamata a ɗauki ɗan takarar shugaban dake ɓoye rashin lafiyarsa dagaske ba.
Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, shi ne ya faɗi haƙa yayin da yake martani kan kalaman da ɗan takarar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin taronsa da Malaman Ɗarikar Tijjaniyya a Kano.
Asali: Legit.ng