Najeriya Za Ta Wargaje Idan Tinubu da APC Suka Ci Zabe a 2023, Inji Gwamnan PDP Obaseki

Najeriya Za Ta Wargaje Idan Tinubu da APC Suka Ci Zabe a 2023, Inji Gwamnan PDP Obaseki

  • Gwamnan jihar Edo ya fadi kadan daga illolin jam'iyyar APC da kuma asarar da za ta jawowa Najeriya idan ta koma mulki
  • Daga cikin ya ce, APC za ta jawo wargajewar Najeriya domin ta riga ta lalata komai, ana bukatar wanda zai kawo gyara
  • Kana ya tono asirin APC, ya tana buga kudi kuma tana yawan cin bashi da sunan Najeriya, lamarin da zai yiwa kasar wahala nan gaba

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya gargadi 'yan Najeriya a ranar Litinin cewa, idan suka sake APC ta sake komawa mulki, to tabbas kasar za ta wargaje.

Obaseki ya bayyana hakan ne a bikin kaddamar majalisar kamfen din jam'iyyarsu ta PDP a jihar, kamar yadda Channels Tv tace ta samo.

Kara karanta wannan

Kalaman Wani Gwamnan PDP Kan Kamfen Atiku Ya Tada Kura, An Nemi Ya Yi Murabus

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, babu wanda notunan kansa ke daure da zai amince ya zabi Tinubu da APC a zaben da za a yi nan da watanni hudu a kasar nan.

Gwamna Obaseki ya fadi kadan daga illar gwamnatin APC
Najeriya Za Ta Wargaje Idan Tinubu da APC Suka Ci Zabe a 2023, Inji Gwamnan PDP Obaseki | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yadda gwamna ya caccaki APC

Ya shaidawa Channels Tv cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan zabe ne mai sauki idan muka yi gangamin kamfen yadda ya dace saboda a zahirin gaskiya ya kamata a duba kawunanmu a matsayinmu na 'yan Najeriya idan muka yi tunanin zaben gwamnati kamar ta APC.
"Kai, kamar ma yadda na fada, Allah ya kare APC ta sake mulki, kasar nan za ka wargaje, kasar nan za ta fadi amma tuni dama ta fadi saboda babu wanda ya yiwa kasar nan illa kamar APC. Ban san ta yaya za mu dawo daidai ba.
"Zuciyata na bugu. Idan Atiku ya hau mulki, to bacci ya kare, za mu yi aiki ba rana ba dare. Da nake magana daku a yau, bashin kasar nan zai haura zuwa tiriliyan 60, yaushe za mu warware wannan? Kowacce rana, kowane wata buga kudi suke yi."

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

2023: Nan Ba Da Jimawa ba Yan Obidient Zasu Gaji, Ba Inda LP Zata Je, Obaseki

A wani labarin, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kore duk wata damar samun nasara ga jam'iyyar Labour Party da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a babban zaɓen 2023.

Channels TV ta rahoto cewa Obaseki ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen jam'iyyar PDP na jiharsa ranar Litinin.

Gwamnan yace mabiyan Peter Obi waɗanda suka yi ƙaurin suna da "Obidients" nan ba da jimawa ba zasu rasa wannan tururin da zumudin da suke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel