Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

Sunan Darektan Kamfe a APC Ya Fito a Kwamitin Yakin Neman Zaben Peter Obi

  • Dr. Nasir Danladi Bako yace ba sunan shi aka gani a ‘yan kwamitin neman zaben jam’iyyar LP ba
  • Akwai sunan wani Mr. Danladi Bako a kwamitin wadanda za su taya Peter Obi kamfe a takarar 2023
  • ‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa har gobe yana nan a APC, kuma bai da wani hadi da tafiyar su Obi

Abuja - Danladi Bako wanda shi ne Darektan dabarun yada labarai na kwamitin yakin takarar shugaban kasa a APC ya cire mutane daga duhu.

An ga sunan Danladi Bako a cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta LP duk da yana tare da APC mai mulki.

A jerin wadanda za su taya Peter Obi samun nasara a zaben shugaban kasa, an ga sunan ‘Danladi Bako’ a matsayin shugaban kamfe na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Bayan An Kai Ruwa Rana, Gwamna Wike Ya Yarda Zai Marawa Atiku Baya da Sharadi

A wani jawabi da ya shigo hannun jaridar The Cable, Mista Bako yace ‘Danladi Bako’ da aka gani a jerin mai kunshe da mutane 1234 a LP ba shi ba ne.

Takwara na ne, ba ni ba - Bako

‘Dan siyasar yake cewa akwai wasu masu irin sunansa, yace an yi dace ne kurum aka samu wani takwaransa da yake yi wa Obi aiki a zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto Dr Nasir Danladi Bako a ranar Alhamis yana cewa babu abin da ya hada shi da tafiyar Obidient.

Peter Obi
'Dan takaran LP, Peter Obi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

“Hankali na ya zo ga wasu sunaye da yake yawo, dauke da jagororin kwamitin yakin zaben jam’iyyar Labour Party
A jerin akwai wani Mista Danladi Bako a matsayin shugaban kamfe na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Daga Fitar da Sunayen ‘Yan Kwamitin Zabe, An Fara Rigima a Jam’iyyar LP

Ni, Dr Nasir Danladi Bako, ina so in fada da babbar murya cewa akwai wasu mutanen da suke da suna irin nawa.
Saboda haka jawabin da nake yi shi ne, ba ni Dr. Nasir Danladi Bako PhD OON ne a cikin jerin wadannan sunayen ba.”

.....Yace

Kwamitin 'yan kamfe ya jawo magana

Tun da kwamitin yakin neman zaben Peter Obi ya fitar da sunayen jagororin takara ake ta surutu, ana zargin akwai karancin ‘yan Arewa a kwamitin.

Mun fahimci an koka da ganin sunan Janar John Enenche. Enenche ya karyata cewa an kashe mutane a rikicin EndSARS a lokacin yana gidan soja.

NNPP za ta samu kuri'u miliyan 5 a Kano

An ji labari Dr. Abdulmumuni Jibrin Kofa ya karbi mutane 2000 a Jam’iyyar NNPP, har ya sha alwashin kawowa Rabiu Kwankwaso kuri’u masu yawa.

Shahararren ‘dan siyasar ya yi alwashin ganin Kwankwaso ya tashi da kuri’u miliyan biyar daga garuruwan jihar Kano a zaben shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Jam’iyyu Sun Tona 'Kullaliyar' da Ake Yi Na Canza Shugaban INEC da Birkita Zaben 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel