Za a Tarawa Kwankwaso, NNPP Kuri’u Miliyan 5 a Jihar Kano a Zaben Shugaban kasa

Za a Tarawa Kwankwaso, NNPP Kuri’u Miliyan 5 a Jihar Kano a Zaben Shugaban kasa

Hon. Abdulmumuni Jibrin ya yi alkawari Rabiu Musa Kwankwaso zai samu kuri’u miliyan 5 a Kano

Kofa yake cewa za su shiga lungu da sako domin tallata ‘dan takaran shugaban kasar NNPP a jihar

Shi ma Jibrin yana sake neman kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na Kiru/Bebeji a 2023

Kano – Hon. Abdulmumuni Jibrin mai neman takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Kiru/Bebeji ya soma yakin zaben shekarar 2023.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Talata, Abdulmumuni Jibrin ya sha alwashin ganin jam’iyyar NNPP ta samu nasara a jihar Kano.

Jibrin yace za su dage domin ganin Rabiu Musa Kwankwaso mai neman takarar shugabancin kasa a NNPP ya samu kuri’a miliyan biyar a mahaifarsa.

Kara karanta wannan

An Nemi ‘Dan Tsohon Shugaban Najeriya ya zama Mataimakin Peter Obi, Ya ki Yarda

‘Dan siyasar ya tara jama’a a garin Kofa da ke Kiru a wani babban gangamin siyasa da ya shirya, inda ya karbi mutum 2000 da suka shigo jam’iyyar NNPP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda Blueprint ta fitar da rahoto, tsohon ‘dan majalisar ya yi wankan tsarki ga wadanda suka baro wasu jam’iyyu, suka zabi mai alamar kayan dadi.

Da yake yi wa mabiyansa jawabi a wajen taron, ‘dan siyasar ya yi kira ga jama’a su guji yin zaben tumin-dare, domin hakan zai kara jefa kasar a matsala.

Kwankwaso mai neman Shugaban kasa
Hon. Abdulmumini Jibril yana tare da Kwankwaso Hoto: @AbdulAbmJ
Asali: Twitter

Na fara kamfe - Jibrin

Na fara yakin neman zabe a mazabata ta Kiru da Bebeji a Kano a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba 2022.
Za mu dukufa da yakin neman zabe lungu-lungu domin ganin Kwankwaso ya samu kuri’u miliyan 5 a Kano.
Allah SWT Ya bamu sa;a, amin #RMK2023 #AbbaGidaGida2023 #Kawu2023 #AJKofa2023 #NNPPNewNigeria

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Bayyana Abubuwa 2 da Zai ba Muhimmanci Idan Ya Samu Mulki

Kuri'a miliyan 5 za su fito?

Daga baya sai aka ji Mashood Shitu, daya daga cikin jagororin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kwara yana maimata irin maganar Abdulmumini Jibrin.

Mashood Shitu yake magana a shafin Twitter, yace a Kano kurum, ‘dan takaran na NNPP zai samu kuri’a miliyan biyar domin ya kara samun mabiya.

Ba mu tsoron NNPP - Sanata Gaya

Duk da Hon. Kawu Sumaila ya samu takara a Jam’iyyar NNPP, an ji labari Sanata Kabiru Gaya ya kore nasara daga hannun PDP da ita NNPP a Kano.

‘Dan majalisar wanda yana cikin na-hannun daman Yemi Osinbajo a lokacin da ya nemi tikitin kujerar shugaban kasa, yace APC za tayi galaba a badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel