Inyamurai Na Da Duk Abin Da Ake Bukata Na Mulkar Najeriya, Inji Gwamna Samuel Ortom

Inyamurai Na Da Duk Abin Da Ake Bukata Na Mulkar Najeriya, Inji Gwamna Samuel Ortom

  • Gwamnan jihar Benue ya bayyana kwarin gwiwarsa kan kabilar Inyamurai mazauna jiharsa dake Arewacin Najeriya
  • Ya bayyana cewa, Inyamurai na da dadin zama, kuma sun fi Fulani makiyaya dake kashe 'yan uwansa a a cewarsa
  • Ya kuma bayyana cewa, Inyamurai na da duk abin da ake bukata na kawo mafita ga duk wasu matsalolin Najeriya

Makurdi, jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa, al'ummar Inyamurai na da duk abin da ake bukata su mulki Najeriya matukar aka basu dama.

Gwamnan ya kuma kara da cewa, Inyamurai na da kwarewa da gogewar iya habaka tattalin Najeriya idan suka samu dama.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin jiharsa dake Makurdi yayin da 'yan kabilar Inyamurai daga mambobin PDP suka kai masa ziyara , Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

Gwamna Ortom ya yabawa Inyamurai, ya ce za su iya mulkin Najeriya
Inyamurai Na Da Duk Abin Da Ake Bukata Na Mulkar Najeriya, Inji Gwamna Samuel Ortom | Hoto: leadershipi.ng
Asali: UGC

Ya yaba musu da cewa, su al'umma ne masu son habaka tattalin arziki da zamantakewa da kawo ci gaba a jiharsa da ma kasar baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ji dadi tare da yaba irin goyon bayan da suka bayar a jiharsa da ma kasa, inda yace sun shajja'a mutane da dama, ciki har da shi kansa, rahoton New Telegraph.

Inyamurai a idon gwamnan jihar Benue

A cewarsa:

"Al'ummar Inyamurai suna da dadin zama kuma masu aiki tukuru ne. Su gungun mutane da ke iya zama lafiya da sauran kabilu ba irin wadancan dake kashe mutane na ba kuma suke son na yi shuru.
"Ba zan taba shuru game da hare-hare ba gaira ba dalili akan mutane na daga makiyaya ba har ai hukumomi sun yi abin da ya dace. Zan ci gaba da magana akan rashin adalci."

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Ya kuama kara da cewa:

"Babu wanda ya isa ya yi barazana ga tikiti na na sanata. Mutum ba zai samu komai ba har sai Allah ya bashi, ina son yabawa Inyamurai a Benue da ma kewayen jihar bisa dabaru da karfafa matasa wanda shine abu na farko da ake bukata."

Ta kwabewa APC da Tinubu, mambobin APC 2000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

A wani labarin, a ranar Laraba 12 ga watan Oktoba ne wasu mambobin APC akalla 2000 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP ta dawa a jihar Yobe.

A cewar mambobin da suka saki APC, ba za su ci gaba da zama a jam'iyyar da Buhari ya yi alkawari amma ya gaza cikawa ba, haka nan gwamnansu Mai Mala Buni.

Sabbin mambobin na jam'iyyar PDP sun kuma bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabe mai zuwa, Rivers Mirror ta tabbatar.

Kara karanta wannan

EFCC ba za su iya yakar rashawa ba a Najeriya, dan takarar shugaban kasa ya fadi dalili

Asali: Legit.ng

Online view pixel