Yadda Kanin Miji Ya Kwace Matar Dan Uwansa Mai 'Ya'ya Bakwai

Yadda Kanin Miji Ya Kwace Matar Dan Uwansa Mai 'Ya'ya Bakwai

  • Simon Murefu Muyeho ya yi da'awar cewa, matarsa Farida wacce suke tare na tsawon shekaru ta yi watsi dashi ta kama kaninsa
  • A cewarsa sun haifi 'ya'ya bakwai tare, wadanda a yanzu suke rayuwa babu uwa kuma shi yake ci gaba da fafutuka dasu
  • Mutumin dan kasar Kenya ya ce, matarsa ta kamu da son kaninsa ne saboda yana daukar ta a babur kasancewar yaan sana'ar acaba

Kenya - Wani mutum mai shekaru 56 ya bayyana irin wahalar da yake sha na kula da yara bakwai da matarsa ta bar masa bayan da ta tare da kaninsa.

Simon Murefu Muyeho ya ce, kaninsa dan acaba ne, yakan dauki matarsa Farida a babur har soyayya ta kullu a tsakaninsu.

Yace, yayin da kusancinsu ya yi nisa, Farida ta bayyana soyayyarta ga kaninsa, wanda suka koma zama tare a karkashin rufi daya.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Kanin miji ya kwace matar dan uwansa, rikici ya tashi
Yadda kanin miji ya kwace matar dan uwansa mai 'ya'ya bakwai | Hoto: Afrimax English
Asali: UGC

Ya shaidawa AfriMax cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Nakan bibiyi lamarin, nakan cewa kanina ya dawo min da matata, amma ya ki. Duk da haka, ba zan fidda rai ba game da matata. Idan haka ya ci gaba da faruwa, zan tunkari hukumomi domin warware matsalar."

A cewar mutumin, kullum kaninsa na nuna bai tare da Farida, amma a zahiri ba gaskiya bane, domin kuwa kullum akan gansu tare.

Ya kuma shaida cewa, kanin nasa yakan sauya wuraren zama daga gari zuwa wani garin saboda kada a gane inda suke.

Martanin matar da ake rikici a kanta

Sai dai, a nata bangaren, Farida, wacce 'yar kasuwa ce ta bayyana cewa, mijin nata na musguna mata.

Ta ce:

"Ya cika fada. yakan suburbude ni duk lokacin da ya dawo daga aiki. Yana sana'ar gadi ne kuma yakan dawo gida ne da safe a buge bayan ya sha taba da barasa. Ya ma kusan kashe ni, amma kwanana na gaba, saboda yana zargin ina masa kwange.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri

"Ya taba kona ni, ya kuma karya min hannu. Wannan yasa nake da nakasa. Sai dai yunwa ta karmu matukar ban nema abin da zamu ci ba. Mutum ne mara kamun kai."

An hana ta ganin 'ya'yanta

Farida ta kuma bayyana cewa, mijin nata ya haramta mata ganin 'ya'ya bakwai da suka haifa tare bayan ta zabi zama da kanin mijinta.

Ta ce tana kaunar kanin mijin nata saboda ya san yadda ake tafiyar da mace da biyan bukatunta.

Shi kuwa kanin mijin Farida cewa ya yi, matar ba ta cikin kwanciyar hankali a zamanta da dan uwansa, don haka ya samu damar zama da ita.

Bidiyon Wata ‘Yar Najeriya Ta Mutu Yayin da Ake Yi Mata Cikon Mazaunan Roba a India

A wani labarin, wata tsaleliyar budurwa 'yar Najeriya mai shekaru 28, Amelia Pounds ta riga mu gidan gaskiya yayin da yi mata aikin gyaran jiki a kasar India.

Kara karanta wannan

Son gaskiya: Soyayya ta sa wata kyakkyawar mata ta auri makaho, bidiyonsu ya ba da mamaki

An ruwaito cewa, budurwar 'yar kasuwa ta sheka ne yayin da ake kan yi mata tiyatar cikon mazaunai a wani asibitin da a bayyana sunansa ba a birnin New Delhi a ranar Juma'a 7 ga watan Oktoba da safe.

Wani mai amfani da shafin Twitter ya tabbatarwa wata ma'abociya kafafen sada zumunta, Vera Sidika labarin, inji kafar labarai ta Linda Ikeji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel