Tsohon Gwamnan da Aka Daure Yace Obasanjo Ya Ci N100m Cikin Kudin Sata

Tsohon Gwamnan da Aka Daure Yace Obasanjo Ya Ci N100m Cikin Kudin Sata

  • Joshua Dariye ya yi bayanin yadda aka batar da N1.1bn da ake zargin ya sace a sa’ilin yana mulki
  • Tsohon gwamnan na Filato yace ya kashe N100m a cikin kudin domin taimakawa Olusegun Obasanjo
  • Sanata Dariye ya yi ikirarin N166m sun shiga asusun jam’iyyar PDP, yace N4m ne kurum suka bace

Plateau - Tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye ya yi bayanin yadda ya batar da wani bangare na kudin da aka kama shi da laifin karkatarwa.

The Nation ta rahoto Sanata Joshua Dariye yana cewa yakin neman zaben 2003 ya ci Naira miliyan 100 daga cikin N1.126bn da ya yi awon gaba da su.

A cewar Joshua Dariye, ya kashe Naira miliyan 100 ne domin a taya Olusegun Obasanjo yakin neman tazarce a lokacin yana shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan Arewa Da Buhari Ya Yi Wa Afuwa Ya Fadi Yadda Za'a Kawo Karshen Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Bayan ya bar kujerar mulki a 2007, hukumar EFCC ta zargi Dariye da laifin satar N1.126b daga asusun gwamnatin jihar Filato, tayi karar shi a kotu.

Sai a 2018 babban kotun tarayya ta yankewa tsohon gwamnan hukuncin daurin shekaru 14. Kotun daukaka kara ta rage hukuncin zuwa shekara 10.

A shekarar bara, kotun koli ta tabbatar da hukuncin da Alkalan suka yi, wannan ya sa aka rufe Dariye a kurkuku, kafin gwamnati tayi masa afuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Joshua Dariye, Olusegun Obasanjo
Hoto: Olusegun Obasanjo da Joshua Dariye
Asali: Facebook

Joshua Dariye ya yi bayani

Da aka tattauna da shi a wani shiri na “Newsnight” a gidan talabijin Channels TV a ranar Litinin, Dariye ya yi bayani dalla-dalla kan aka kashe kudin.

Sanata Dariye yace a cikin wadannan makudan kudi, Naira miliyan hudu ne ba a gani ba.

The Cable ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa siyasa tayi aiki wajen daure shi. A hirar da aka yi da shi, ya koka kan halin da ya samu gidajen yarin kasar.

Kara karanta wannan

2023: Wanda Atiku Ya ba Mukami, Ya Watsa Masa Kasa a Ido, Yace Ba Zai Karba ba

Ina aka kai N1.12bn?

“N800m ya shiga asusun jihar Filato; N100m ya je hannun jam’iyyar PDP ta Kudu maso yamma, sai wasu N100m suka tafi kwamitin yakin zaben Obasanjo.
N80m ya je asusun kula da muhalli, sai aka tura N66m ga PDP ta reshen jihar Filato. Abin da aka nema aka rasa N4m, wanda wannan kwamashon kudin ne."

- Joshua Dariye

EFCC: Dalilin sauke Magu

An ji labari cewa Mohammad-Saeed Ibrahim Magu ya wakilci mahaifinsa Ibrahim Magu wajen biki da aka karrama tsohon shugaban hukumar EFCC.

Tsohon shugaban EFCC na rikon kwarya yace yakar barayi ya yi sanadiyyar rasa aikinsa, amma yace ga shi tun yanzu gaskiya ta fara nuna halinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel