Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

  • Chris Ngige yaki fitowa fili ya lamuncewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa a zaben 2023 duk da matsin lambar da ya sha
  • Ministan kwadagon ya bayyana cewa zai bayyana matsayinsa idan ya isa gaban akwatin zabe don kada kuri'arsa a 2023
  • Sai dai kuma, ya tabbatar da cewar Bola Tinubu yayi namijin kokari a lokacin da yayi gwamnan jihar Lagas

Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, yace ba zai bayyana dan takarar shugaban kasa da yafi so ba a zaben 2023.

Ngige ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya bayyana a shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin din Channels.

Christ Ngige
Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023 Hoto: Chris Ngige
Asali: Twitter

Da aka tamabaye shi game da wanda zai marawa baya tsakanin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa, da Peter Obi na Labour Party, Ngige ya bayyana tambayar a matsayin mai wahala.

Kara karanta wannan

Ba harka: Dan takarar shugaban kasan wata jam'iyya ya tsorata, zai janye daga takara

“Na fada maku cewa ni bana cikin harkar siyasa dumu-dumu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bana siyasa a halin yanzu saboda na fuskanci aikin kasa da aka rataya mun a wuya.
“Su duka biyun abokaina ne. Zabina zai bayyana ne a akwatin zabe. Imma daidai ko ba daidai ba, a wannan rana a watan Fabrairu, zan zabi mutum daya.”

Ministan ya kara da cewa:

“Zaben sirri ne, bai kamata na fadawa yan Najeriya abun da zan yi a sirrince ba.
“Su dukka mutanen biyu suna da tarihinsu mai kyau, amma dole sai ka duba ina yafi muhimmanci a nazarinka.
“Asiwaju Bola Tinubu ya zo Lagas lokacin da babu komai. Na zauna a Lagas don haka zan iya fada maku. Yayi abun da ya kamata yayi sannan ya gyara tsarin kudin, ya gina tubali mai inganci da matattakala ga magajinsa.”

Kara karanta wannan

Allah Ya Wadarar A Sake Baiwa PDP Amanar Baitul Malin Al'umma, Lai Mohammed

Ngige yace Obi ya gina kan tubalin da ya shimfida a matsayin gwamnan jihar Anambra.

“A zangon farko, bai yi ababen more rayuwa ba, amma sai ya gano cewa hakan babban kuskure ne.”

Da aka nemi ya kimanta kokarin Tinubu ko yafi na Obi, ministan yayi burus, rahoton TheCable.

Ga bidiyon tattaunawar a kasa:

Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

A wani labarin, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta bayyana cewa gwamnoni 18 a fadin jam’iyyun siyasa da kabilu daban-daban suna goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, PM News ta rahoto.

Kungiyar Inyamuran ta bayyana cewa wannan dandali ya zama na yan Najeriya masu muradin ganin an ceto kasar daga mawuyacin hali da take ciki ta bangaren tattalin arziki da zamantakewa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya gabatarwa manema labarai a ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel