Shugabannin APC 16 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Sakkwato Gabanin 2023

Shugabannin APC 16 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Sakkwato Gabanin 2023

  • Yayin da 'ya'yan jam'iyyar APC ke murnar dawowar Bola Tinubu, jam'iyyar ta yi rashin wasu shugabanninta na matakin gunduma a Sakkwato
  • Wasu shugabannin APC a gundumomi biyu dake karamar hukumar Sabon Birni sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ranar Jumu'a
  • Masu sauya shekar sun sha alwashin aiki tare sa masu fada a ji na PDP don tabbatar da jam'iyyar ta yi nasara a zaben 2023

Sokoto - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, aƙalla shugabannin jam'iyyar APC a matakin gunduma 16 suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP a jihar Sakkwato ranar Jumu'a.

Da yake jawabi yayin karɓan masu sauya shekar a gidansa na Sakkwato, shugaban PDP na jiha, Alhaji Bello Goronyo, ya ba su tabbacin cewa sun zama ɗaya da kowa ba zancen nuna banbanci.

Kara karanta wannan

2023: "Da Sauran Matsala" Jigon PDP Ya Fallasa Gaskiyar Abinda Ya Faru a Taron Wike da BoT

APC da PDP.
Shugabannin APC 16 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Sakkwato Gabanin 2023 Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch ta ruwaito a jawabinsa yana cewa:

"A jam'iyyar PDP, muna ɗaukar kowane mamba dai-dai da kowa, a ko da yaushe muna tsaya wa kan sunanmu domin mutane, bisa haka ina baku tabbacin cewa zamu yi aiki tare domin kyaun goben jihar mu da ƙasa baki ɗaya."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Matakin da kuka ɗauka na haɗa kai da mu a tafiyar da muka sa a gaba babban cigaba ne a wurin mu jagorori kuma ina da yaƙinin cewa shigowarku zai kara mana karfin nasara."

A wata sanarwa da Hassan Sahabi Sayinnawal ya raba wa manema labarai, shugaban PDP na jiha ya kara da rokon masu sauya shekan su ci gaba da ilimantar da mutane dumbin ayyukan alherin da gwamantin Aminu Waziri Tanmbuwal ta aiwatar a jihar.

Meyasa suka yanke fita daga APC?

Da yake jawabi a madadin sabbin mambobin, Alhaji Garba Dan Sanda, yace sun yanke shiga PDP ne saboda namijin kokarin da suka ga gwamnati mai ci na yi wajen kawo ci gaba a fadin sassan jihar.

Kara karanta wannan

Fushin Gwamnoni: Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Dan Sanda ya tabbatar da cewa baki dayansu zasu yi aiki kafada da kafada da jagororin jam'iyyar PDP a matakin gunduma, kananan hukumomi da jiha domin tabbatar da nasara a babban zaben 2023.

Bugu da kari ya yaba wa shugabannin PDP bisa tarbansu hannu bibbiyu da kuma kara musu kwarin guiwar shiga a dama da su wajen fafutukar tunkarar babban zaben dake tafe, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Yan siyasan da suka sauya sheka

Daga cikin jiga-jgan APC da suka sauya shekar sun hada da' Aliyu Liman, Adamu Salihu, Alinbo Dan-Tudu, Abdullahi Belbela, Abdu Langebo, Hussain Langebo da kuma Umaru Dadi.

Sauran sune Abubakar Isa, Agada Lajinge, Usman Kalla, Isa Suleiman, Yawale Isa, Jadi Abdullahi da Aminu Makuwana, dukkansu daga gundumar Lajinge da Makuwanaa karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sakkwato.

A wani Labarin kuma Jiga-Jigai da Mambobin APC Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kogi

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Rashin Aikin Yi Cikin Matasa Ka Iya Haifar da Tarzoma A Kasa

Mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa Peoples Democratic Party(PDP) a jihar Kogi.

'Yan siyasan sun koma PDP ne ranar Lahadi a gundumar Avrugo da wata maƙotanta, ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu da ke jihar dake shiyyar arewa ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel