Jam'iyyar APC Ba Zata Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Idan Babu Gwamnoni, Adamu

Jam'iyyar APC Ba Zata Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Idan Babu Gwamnoni, Adamu

  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, yace idan har gwamnoni suka zare hannunsu jam'iyyar ba zata kai labari ba a 2023
  • Tsohon gwamnan jihar Nasarawa yace nasarar APC na hannun Allah kuma tana hannun gwamnoni
  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, yace Sanata Adamu ya kira taro ne domin tattauna batutuwan da suka shafi APC

Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, yace jam'iyyar ba zata kai labari ba a zaɓen 2023 matukar gwamnonin jam'iyyar basu mara mata baya ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya yi wannan furucin ne yayin jawabin buɗe taron gwamnoni, mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) da masu ruwa da tsaki a Sakatariyar APC ta kasa dake Abuja ranar Laraba.

Taron ƙusoshin APC.
Jam'iyyar APC Ba Zata Kai Labari Ba a Zaben Shugaban Kasa Idan Babu Gwamnoni, Adamu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba gwamnonin sun nuna fushinsu a fili kan tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda Sakatare, James Falake, ya saki a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Muhimmin Abun Da Zan Yi Idan Na Ɗare Kujerar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 2023, Kwankwaso

Biyo bayan rikicin da ya kunno kai, Darakta janar na tawagar Kamfen kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ɗage fara yaƙin neman zaɓen shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A taron yau Laraba Adamu yace:

"Kasancewar su zababbun shugabanni a jihohinsu, nauyin jam'iyyarmu mai albarka na hannun Allah kuma yana hannunsu saboda sune jagaba wajen sa'ar jam'iyyarmu a jihohinsu."
"Ba zamu je ko ina ba a waɗannan jihohin musamman lokacin da muke tunkarar shekarar zaɓe, ba zamu kulla komai ba tare da gwamnoni ba, ta yadda zamu dunƙule wuri ɗaya da manufa guda."
"Tare ya dace mu shirya mu ga yadda zamu sa kishin jam'iyya a gaba kuma mu tabbatar da nasara ta mu ce a babban zaɓen 2023 da yake ƙara karatowa, wannan ne dalilin kiran taron."

Menene maƙasudin taron na yau?

Da yake jawabi a wurin, darakta Janar na tawagar kamfe, Gwamna Simon Lalong, yace Adamu ya kira taron ne domin tattauna batutuwan da suka shafi cigaban APC.

Kara karanta wannan

2023: Ƙarin Matsala Ga Tinubu, Jigon APC da Wasu Dubbannin Mambobi Sun Koma Bayan Atiku

A wani labarin kuma Uba Sani da Wasu Yan Takara 16 Sun Shiga Jerin Sunayen INEC Na Karshe a Zaɓen Gwamnan Kaduna 2023

Hukumar zaɓe ta ƙasa ta saki sunayen yan takarar gwamnan jihar Kaduna da zasu fafata a babban zaɓen 2023.

Sanata Uba Sani, Isah Ashiru Kudan, Sulaiman Hunkuyi da wasu yan takara 14 sun shiga jerin sunayen INEC na ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel