"Da Sauran Matsala" Jigon PDP Ya Fallasa Abinda Ya Faru a Taron Wike da BoT

"Da Sauran Matsala" Jigon PDP Ya Fallasa Abinda Ya Faru a Taron Wike da BoT

  • Chief Bode George, yace babu ko matsala ɗaya da aka shawo kanta a wurin taron BoT da gwamnan Ribas, Nyesom Wike
  • George, jigo a jam'iyyar PDP kuma ɗaya daga cikin masu neman Ayu ya yi murabus yace BoT ta nuna za'a cigaba da zaman
  • Tun bayan zaɓen fidda gwanin PDP da ya gudana a watan Mayu, jam'iyyar ke fama da rikicin cikin gida

Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Chief Bode George, yace babu batu ɗaya da aka warware dangane da fusatattun mambobin jam'iyyar a wurin ganawar gwamna Wike da kwamitin amintattu.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mambobin BoT na PDP ta ƙasa bisa jagorancin, Sanata Adolphus Wabara, sun zauna da gwamna Nyesom Wike na Ribas domin lalubo hanyar warware rikicin PDP.

Chief Bode George.
"Da Sauran Matsala" Jigon PDP Ya Fallasa Abinda Ya Faru a Taron Wike da BoT Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bode George na ɗaya daga cikin Mambobin jam'iyyar da ke bukatar shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus, domin a cewarsu fasali da tsarin jam'iyyar babu adalci a ciki.

Kara karanta wannan

Fushin Gwamnoni: Shugaban APC Na Ƙasa Ya Faɗi Babban Abinda Zai Sa Tinubu Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Tun bayan ayyana Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shuagabn kasa, wasu kusoshin jam'iyyar suka nemi a maida kujerar shugaban PDP kudancin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsu, sun nemi haka ne bisa hujjar cewa kundin dokokin jam'iyya ya tanadi yin adalci da kuma dai-daito.

Wace matsaya aka cimma a taron Wike da BoT?

Da aka nemi ya yi tsokaci kan taron a wata hira da kafar Talabijin ɗin Channels cikin shirin Sunrise Daily, Mista George yace:

"Bana cikin mahalarta taron, amma bayanan da na tattara daga baya sun nuna cewa batutuwan da aka tattauna waɗanda sune muka nuna damuwa akansu ba'a warware su ba."
"Kuma kwamitin bisa jagorancin Sanata Wabara sun bayyana cewa za'a ci gaba da zaman. Maganar gaskiya dama ya rataya a wuyan BoT su shiga tsakani kuma ina da tabbacin zasu koma su zauna da waɗanda suka ƙagara a nemo masalaha."

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

A wani labarin kuma Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa babu jam'iyyar da ta kai PDP a duk faɗin Najeriya

Mai neman zama shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yace babu jam'iyya a Najeriya da ta zarce PDP ta ko wane fanni.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya samu kyakkyawar tarba daga cincirindon magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel