Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

  • Jam’iyyar APC da magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu cike suke da murna da dawowar ‘dan takaran
  • Asiwaju Bola Tinubu ya shigo Najeriya bayan ya shafe tsawon kwanaki 12 yana zaune a birnin Landan
  • Ana sa dawowar ‘Dan takaran jam’iyya mai-mulkin ya sa APC ta shiga neman zaben 2023 gadan-gadan

Abuja – Jirgin Asiwaju Bola Tinubu mai neman kujerar shugaban kasa a Najeriya ya dura babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke garin Abuja.

Da yake jawabi bayan isowarsa, ‘dan siyasar ya tabbatarwa mutanen kasar nan cewa abin fatansu ya dawo, bayan jama’a sun fara cire rai da tsammani.

Vanguard ta rahoto tsohon gwamnan na jihar Legas yana cewa ya yi murnar dawowa kasarsa ta gado, tare da kira na musamman ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana Sauraron Dawowar Bola Tinubu Najeriya a Yau Dinnan Inji Hadimin Buhari

A wani bidiyo da yake kafafen sada zumunta, an ji Bola Tinubu yana cewa ya dawo da karfinsa.

“Tafiyar tayi kyau sosai, na ji dadin hutu na, kuma ina farin cikin dawowa kasa ta.
Mutanen Najeriya su sa tsammanin ganin basira wajen tunani da tabuka aiki. ‘Yan Najeriya su sa ran cewa taimakon da suke bukata ya zo gare su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Fatan da ake da shi wanda ya kusa kubucewa ya dawo. Na dawo da karfina.”

- Bola Tinubu

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: Ayekooto Akindele
Asali: Facebook

Kishin kasa

A jawabinsa, an rahoto Tinubu yana kira ga al’umma su zama masu kishin kasarsu, su daina fadar munanan abubuwa a game da halin da Najeriya take ciki.

‘Dan siyasar yace idan ana bukatar a gina kasar ne, to shi magini ne. Haka zalika yace idan gyara ne kasar take bukata, shi kwararren mai gyaran gini ne.

Kara karanta wannan

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

Martanin Festus Keyamo

Da yake magana a kan dawowar ‘dan takaransu, Festus Keyamo yace jam’iyyun adawa sun gaza fara shirin yakin neman zabe, suna sauraron Tinubu.

"Jam’iyyun hamayya suna jiran shi (Bola Tinubu) domin su soma yakin takara.
A maimakon su tallata ‘yan takaransu, sun buge da tambayar ‘Ina BAT?! To, ga shi nan ya dawo, sai su fara (kamfe).

- Festus Keyamo

Atiku ya kara Darektoci

Watanni bayan ya yaki Atiku Abubakar a takarar tsaida gwani, an ji labari Bashorun Dele Momodu ya zama Darektan kamfe na PDP a zaben 2023.

Manyan ‘Yan PDP kamar su Baraka Sani, Hon. Umar M. Bature da Kamaldeen Ajibade SAN duk sun shigo jirgin kamfe da kyau a matsayin darektoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel