Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

Iyorchia Ayu Ya Dawo da Zafinsa, Ya Bukaci Ayi Bincike Kan Shugabannin Jam’iyya

  • Bayan dawowarsa daga ganin Likita a kasar waje, Iyorchia Ayu ya jagoranci zaman NWC
  • Dr. Ayu da ‘yan majalisarsa sun tattauna a kan batun wadanda suka maida kudi a asusun jam’iyya
  • Kamaludeen Ajibade SAN zai gudanar da bincike na musamman wanda za a gabatarwa NWC

Abuja - Mako guda kenan daga dawowarsa daga asibiti a kasar waje, shugaban PDP watau Dr. Iyorchia Ayu ya jagoranci wani zama a ranar Talata.

This Day tace taron da ‘yan majalisar NWC su kayi a ranar 4 ga watan Oktoban 2022, ya yi zafi.

Wadanda suka halarci zaman majalisar gudanarwar sun hada ‘yan NWC da suke goyon bayan a cire Sanata Iyorchia Ayu daga mukamin da yake kai.

Timothy Osadolor yace shugabannin PDP na duk shiyyoyin kudancin Najeriya Taofeek Arapaja, Dan Orbih da Stella Effah-Attoe sun je wajen taron.

Kara karanta wannan

Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

Wadanda suka dawo da kudi

Majiya ta shaidawa Punch cewa makasudin taron makon nan shi ne ayi bincike a kan abin da ya faru har Taofeek Arapaja sun dawo da makudan kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Arapaja da wasu abokan aikinsa a NWC sun dawo da N122.4m da suka ce jam’iyya ta aika masu a cikin asusunsu a lokacin shirin zaben tsaida 'dan takara.

Iyorchia Ayu
Shugaban PDP, Iyorchia Ayu Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Duka ‘yan NWC sun halarta. Na fahimci abin kunyan da wasu shugabannin jam’iyya na kasa su shida suka jawo yana cikin abin da aka zauna a kai.
A matsayin shugaba na kasa, ina sane da cewa tsarin mulkin jam’iyya ya hana wani jami’i ya fito yana kokarin tozara jam’iyya kamar irin yadda suka yi."

- Majiya

An ba Kamaludeen Ajibade SAN aiki

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar da jawabi yana cewa Kamaludeen Ajibade SAN zai binciki zargin da wasu ‘Yan NWC ke yi.

Kara karanta wannan

An Sake Duba Sunayen Kwamitin Kamfen din Tinubu, Adamu ya ki Halarta

Ajibade SAN shi ne babban mai ba jam’iyyar PDP shawara a Najeriya kuma wanda zai yi binciki kan lamarin, ya mika rahoto ga NWC a cikin makon gobe.

'Yan takaran Gwamna

A jiya aka ji Hukumar Independent National Electoral Commission (INEC) tace ‘yan takara 10, 200 suke neman zama Gwamna da Mataimakin gwamna.

An fahimci APC za ta shiga takara a jihar Ogun ba tare da hamayya daga PDP da LP ba, watakila hakan ya jawo jam’iyya mai mulki ta ci banza a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel