Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP Ya Samu Mukami a Kwamitin Neman Zabensa

Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP Ya Samu Mukami a Kwamitin Neman Zabensa

  • Kwamitin NCMC mai aikin kula da yakin neman zaben PDP ya nada wasu sababbin Darektoci
  • Wadannan Darektoci da mataimakansa za su taimakawa Atiku Abubakar a zaben shugaban Najeriya
  • Kwararren ‘dan jaridar nan Dele Momodu wanda ya nemi tikitin PDP yana cikin wadanda aka zaba

Abuja - Babban kwamitin da ke kula da yakin neman zabe na NCMC a jam’iyyar PDP, ya nada sababbin Darektoci da kuma Mataimakin Darektoci.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba 2022 cewa kwamitin na NCMC ya zabi wadanda za su taimaka wajen yi masa kamfe.

Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Waziru Tambuwual ya sanar da wannan a wani jawabi.

Kara karanta wannan

Yayin da Aka Hana APC Shiga Takara a Akwa Ibom, Kwankwaso Ya Ci Kasuwa a Jihar

Jawabin yace Rt. Hon. Austin Opara shi ne Darektan horaswa, sai Bashorun Dele Momodu ya zama Darektan harkokin sadarwa na musamman.

An dauko Bature da Ajibade

Gwamnan Sokoto yace kwamitin ya nada Hon. Umar M. Bature da Hon. Abdullahi Hussaini MaiBasira su jagoranci ayyuka a fili da sha’anin kudi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alh. Ibrahim Bashir ya zama Darektan gudanarwa, sai Kamaldeen Ajibade, SAN zai rike Darekta a bangaren shari’a a kwamitin neman takaran 2023.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar wajen bude kamfe Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Baya ga Nurudeen Taoheed Ademola da zai zama Darektan harkokin matasa, akwai Farfesa Iyorwuese Hagher wanda zai jagoranci harkar bincike.

Har ila yau an kawo Janar Koko Essien Rtd da zai rike kwamitin tsaro yayin da Baraka Sani za ta rike da bangaren lura da kungiyoyin magoya.

Sauran darektocin da aka nada su ne: Amb. Ahmed Magaji, Sanyaolu Modupeola, Osita Chidoka, Farfesa Isah Odidi da kuma Hon. Chile Igbawua.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023

Kamar yadda Guardian ta kawo rahoto, ragowar darektocin za su yi aiki wajen shawo kan masu zabe da kuma aiki da mutanen da ke ketare.

Baraka Sani ta taba aiki da shugaban kasa a bangaren noma, shi kuma Osita Chidoka ya jagoranci FRSC kuma ya taba yin Ministan jiragen sama.

Yabon Peter Obi ya jawo an rasa mukami

An samu rahoto Atare Awin ta rasa mukaminta na Mai taimakawa Kwamishina a Delta saboda tayi maganar farin jinin 'Dan takaran LP, Peter Obi.

Anthony Onoriode Ofoni ya fatattaki Atare Awin bayan ya ji tana yabon Peter Obi a shafin Facebook. Kwamishinan ya nuna yana tare da PDP a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel