Diyar Atiku Za Ta Jagoranci Majalisar Kamfen Din Matasan PDP Gabanin 2023

Diyar Atiku Za Ta Jagoranci Majalisar Kamfen Din Matasan PDP Gabanin 2023

  • Gabanin zaben 2023, jam'iyyar PDP ta kawo sabon salo, ta kaddamar da kwamitin majalisar kamfen na matasa a Najeriya
  • Manufar majalisar kamfen matasa na PDP ba komai bane illa tabbatar da matasa maza da mata a kasar nan sun zabi jam'iyyar
  • Daga jiga-jigan da za su jagoranci shirin, akwai Hauwa Atiku Uwais, daya daga 'ya'yan dan takarar shugaban kasa na PDP

Daidai da shirin kwamitin dabaru na kasa (NSC) na PDP, jam'iyyar ta kaddamar da majalisar kamfen din matasa da ta kira NYCC don cimma burin gaje Buhari a zaben 2023.

Majalisar kamfen din jam'iyyar PDP na da burin tabbatar dukkan 'yan takarar PDP sun lashe zabe a fadin kasar nan.

Legit.ng ta tattaro cewa, majalisar ta NYCC za ta dukufa ne gadan-gadan wajen tattarawa da samo kuri'un matasa maza da mata a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Mata a yankin su Peter Obi sun yi biris dashi, sun yi gangamin nuna kaunar Tinubu

PDP ta bayyana sunayen masu mata kamfen daga matasa, har da diyar Atiku
Diyar Atiku za ta jagoranci majalisar kamfen din matasan PDP gabanin 2023 | Hoto: @PDPnewgen
Asali: Twitter

Majalisar za ta yi aiki ne kafada da kafada wajen taimakawa majalisar kamfen din dan takarar shugaban kasa, gwamna, sanata, majalisar dokoki da sauran kujerun siyasa a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda ke shugabantan majalisar

Baya ga wadanda PDP ta ambata a matsayin shugabannin da za su jagoranci tafiyar gangamin kamfen din Atiku, majalisar kamfen na matasa ya kunshi shugabanni kamar haka:

1. Shugabar NSC

Hauwa Atiku-Uwais

2. Darakta janar na NYCC

Audu Mahmood

3. Mataimakin darakta janar na NYCC (Kudu maso Yamma)

Hon. Monsuru Oloyede

4. Mataimakin darakta janar NYCC (Kudu maso Yamma)

Dr. Ugo Williams

5. Mataimakiyar darakta janar NYCC (Kudu maso Kudu)

Cif Misis Shimite Bello

6. Mataimakin darakta janar na NYCC (Arewa maso Yamma)

Hon. Abdullah Abe

7. Mataimakin darakta janar na NYCC (Arewa ta Tsakiya)

Kara karanta wannan

Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci katafaren ofishin kamfen dinsa da aka gina a Abuja

Engr. Shima Ayu

8. Mataimakin darakta janar na NYCC (Arewa maso Gabas)

Hon. Abdulkadir Hashidu

'Yan Sanda Sun Caccaki Wata Jami'a Da Aka GaniTana Dauke da Jakar Matar Atiku

A wani labarin, rundunar 'yan sandan Najeriya ta caccaki abin da wata jami'ar 'yar sanda ta aikata na dakon jakar matar dan takatar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, Punch ta ruwaito.

A wani hoto da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da jami'ar 'yar sandan da ba a tantance sunanta ba ke dauke da jakar Titi Atiku Abubakar a wani taro.

Atiku ne ya yada hoton matar tasa a lokacin da take kaddamar wani shirin mata a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel