Kwankwaso Ya Kai Ziyara Sabon Ofishin Kamfen Dinsa a Abuja

Kwankwaso Ya Kai Ziyara Sabon Ofishin Kamfen Dinsa a Abuja

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna hotunan inda tawagar kamfen dinsa za ta zauna
  • Kwankwaso ya kai ziyara ofishin kamfen din da aka gina a Abuja, ya bayyana cewa nan kusa tawagarsa za ta fara gangami
  • An ba jam'iyyun siyasa damar fara gangami gabanin zaben 2023 da ke gabatowa kuma ke tafe nan kusa

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar duba a wani ofishin kamfen din 2023 nasa da aka gina a Abuja.

Kwankwaso na daya daga cikin 'yan takarar da aka tantance za su gwabza a zaben 2023 mai zuwa domin gaje kujerar Buhari.

Kwankwaso ya kai ziyara ofishin kamfen dinsa
Kwankwaso Ya Kai Ziyara Sabon Ofishin Kamfen Dinsa a Abuja | Hoto: @KwankwasoRM
Asali: UGC

A wasu hotuna da Kwankwaso ya yada a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce da kansa ya je duba aikin da aka yi gabanin jam'iyyarsa ta fara gangamin kamfen dinsa da abokin gamin fasto Idahosa.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Akwai kalaman da Peter Obi ya yi a baya dake nuna yana goyon bayan IPOB

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gabanin fara gangamin kamfen dinmu, an nuna mini hedkwatar gangamin kamfen din Kwankwaso/idahosa dake Abuja.
"Ginin shine zai zama sakatareriyar majalisar kamfen din takarar shugaban kasa dake tafe nan kusa."

Kalli hotunan:

Jam'iyyun siyasa sun fara gangamin kamfen

A ranar 28 ga watan Satumba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta amincewa jam'iyyun siyasa a Najeriya su fara gangamin tallata 'yan takararsu gabanin babban zaben 2023.

Tuni wasu jam'iyyun suka fara yawo tare da fara bayyana manufofin 'yan takararsu dake da burin gaje shugaba Buhari.

Za a zabe a Najeriya a shekarar 2023, kuma tuni hukumomi, 'yan siyasa da jam'iyyu ke ci gaba da shiri.

'Yan IPOB Ba ’Yan Ta’adda Bane, Na Zauna da Su, Inji Peter Obi a 2017

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya taba kakabawa gwamnatin Najeriya laifi wajen ta'azzarar ayyukan barna daga 'yan awaren IPOB.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

Ya kuma ga laifin gwamnati da ta ayyana kungiyar ta su Nnamdi Kanu a matsayin ta 'yan ta'adda, Premium Times ta ruwaito.

A ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ne Peter Obi ya bayyana a gidan talabijin na Channels ya bayyana wadannan maganganu na ganin laifin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel