'Yan Sanda Sun Caccaki Wata Jami'a Da Aka GaniTana Dauke da Jakar Matar Atiku

'Yan Sanda Sun Caccaki Wata Jami'a Da Aka GaniTana Dauke da Jakar Matar Atiku

  • Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta nuna fushi da yadda suka ga wata jami'arsu na dauke da jakar matar Atiku
  • An yi wani taron mata a Abuja, an ga matar dan takarar shugaban kasan PDP na magana a gefen wata 'yar sanda
  • 'Yan sanda na yawan fuskantar kalubalen rashin mutuntawa daga 'yan siyasa da makusantansu a Najeriya

Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta caccaki abin da wata jami'ar 'yar sanda ta aikata na dakon jakar matar dan takatar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, Punch ta ruwaito.

A wani hoto da ya yadu a kafar sada zumunta, an ga lokacin da jami'ar 'yar sandan da ba a tantance sunanta ba ke dauke da jakar Titi Atiku Abubakar a wani taro.

Atiku ne ya yada hoton matar tasa a lokacin da take kaddamar wani shirin mata a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Mata a yankin su Peter Obi sun yi biris dashi, sun yi gangamin nuna kaunar Tinubu

'Yan sanda sun caccaki yadda suka ga 'yar sanda na dakon jakar matar Atiku
'Yan Sanda Sun Caccaki Wata Jami'a Da Aka GaniTana Dauke da Jakar Matar Atiku | Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Yayin da hoton ya zo idon hukumar 'yan sanda, kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ya caccaki abin da jami'ar ta yi kuma yace tabbas za a bincika tare da daukar mataki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar kakakin:

"Wannan abin bai dace ba. Mun fara binciken da ya dace akan wannan. Zamu zakulo ta kuma mu mika ta ga manya. Mun tuntubi sashen kariya na musamman na AIG don taimaka mana wajen gano matar 'yar sanda. A hankali, za mu tsaftace tsarin."

Da yake martani ga hoton, Adejobi ya ce:

"A garemu 'yan sanda, wanna cin mutunci ne kuma bai kamata hakan ya ci gaba da faruwa ba. Gareku, ba lallai ya zama wani abu ba, babban lamari ne saboda dalilai da yawa daga cikin kunsan su da kanku kuma."

Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna

Kara karanta wannan

Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da gwamnonin PDP a Arewa maso Gabas da sauran jiga-jigan siyasar yankin.

Wannan ganawa na zuwa daidai lokacin da Atiku ke ci gaba da samun ciwon kai daga gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan wasu bukatun da ya gabatar ciki har da na sauke shugaban PDP na kasa.

Wadanda suka halarci ganawar da aka yi a yau Laraba 5 ga watan Oktoba sun hada da:

Asali: Legit.ng

Online view pixel