Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

Jam’iyyar PDP Za Ta Kira Taron Gaggawa Domin Ceton Takarar Atiku Daga Watsewa

  • Majalisar amintattu na BoT za tayi zama na musamman a kan rikita-rikitan da ake fama da su a PDP
  • Jam’iyyar PDP tana bakin kokarinta na ganin an dinke duk wata baraka kafin soma kamfen da kyau
  • Manyan jam’iyyar adawar suna so kowa ya marawa takarar Atiku Abubakar/Ifeanyi Okowa baya

Abuja - Idan ba a canza tunani ba, jam’iyyar PDP za tayi zaman a musamman a makon nan, a dalilin irin rigingimun da suke bijiro mata har gobe.

Punch tace majalisar amintattu watau BoT za tayi taro nan da ‘yan kwanaki kadan da nufin a shawo kan rikicin gida saboda a lashe zabe mai zuwa.

Wannan taro yana cikin kokarin da ake yi saboda a magance barakar da za a iya samu wajen takarar Atiku Abubakar a zaben neman shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

Akwai yiwuwar wasu Gwamnoni da kusoshin jam’iyya su kauracewa yakin takarar Atiku a 2023, don haka BoT ke neman yi wa tufkar hanci tun wuri.

Rahoton yace ‘yan majalisar amintattun sun damu da irin sabanin da ake samu tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyya da kuma mutanen Gwamna Nyesom Wike.

Zuwa yanzu babu wanda zai iya cewa ga rana da lokacin da manyan na jam’iyyar PDP za su zauna. Adolphus Wabara ya tabbatar da shirin yin zaman.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

BoT tare da Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
'Yan majalisar BoT a gidan Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Tsohon shugaban BoT ya koka

Da aka tattauna da tsohon shugaban BOT, Sanata Walid Jibrin ya shaidawa ‘yan jarida abubuwan da ke faruwa sun dame su domin sun ki zuwa karshe.

“Akwai taron BoT a makon nan, amma ban san ranar ba tukuna. Abin da muke so shi ne mu ga muna magana da murya daya

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Sannan mu tsaya a kan tsare-tsare da kuma manufofin da za su taimaka mana wajen lashe zaben shugabancin kasa na 2023.
Dole ne mu hada-kan ‘ya ‘yanmu, su jawo mutanen Najeriya domin su fito su zabi Atiku Abubakar da Gwamna Ifeanyi Okowa.”

- Sanata Walid Jibrin

Rikicin Iyorchia Ayu da NWC

Babu mamaki a wannan zama da za ayi, BoT za ta dauki matsaya a kan Sanata Iyorchia Ayu wanda ‘yan bangaren Wike suka huro wuta ya yi murabus.

Walid Jibrin ya kuma yi Allah-wadai da sabanin da ake samu tsakanin ‘yan majalisar NWC. Ana sa ran kwamitin sulhu zai hada Nyesom Wike a yau.

SGF bai goyon bayan Atiku

An ji labari Farfesa Tahir Mamman ya fito yana bayanin asalin abin da ya sa Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha ya je gidan Alhaji Atiku Abubakar.

A wani jawabi na musamman Mamman SAN ya fayyace gaskiyar rade-radin da ke yawo cewa SGF bai tare da Bola Tinubu, yace wannan karyar banza ce.

Kara karanta wannan

Rikicin Kamfe: Tinubu Ya Saduda, Zai Ba APC, Gwamnoni Kujeru 2000 a Kwamitinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel