INEC Ta Saki Sunayen Karshe na ‘Yan Takara, Babu ‘Yan Jam’iyyar PDP da LP a Ogun

INEC Ta Saki Sunayen Karshe na ‘Yan Takara, Babu ‘Yan Jam’iyyar PDP da LP a Ogun

Hukumar Independent National Electoral Commission (INEC) ta wallafa sunayen ‘yan takaran Gwamna

A jihar Ogun, babu wanda aka tsaida a matsayin ‘dan takaran Gwamna da mataimakinsa a PDP

Jam’iyyar hamayya ta LP ba ta ‘dan takara a zaben 2023, amma INEC ta sa sunan APC mai mulki

Ogun - Jam’iyyun hamayya na Peoples Democratic Party (PDP) da Labour Party (LP) ba za su shiga zaben gwamna a jihar Ogun a 2023 ba.

A jerin ‘yan takaran gwamna da hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar, ba a ga sunan wadanda za su yi wa PDP da LP takara a Ogun ba.

Daily Trust tace hukumar zabe ta fitar da sunayen jam’iyyu da ‘yan takara 13 a jerin karshe na ‘yan takara da aka wallafa a Ranar Talatar nan.

Kara karanta wannan

Allah Muke Roko Ya Bamu Mafi Alheri Tsakanin Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso - Sarkin Hausawan Awka

Akwai sunan PDP a rukuni na 21, amma ba a hada da sunan wanda za iyi wa jam’iyyar adawar takarar gwamna da mataimaki a jihar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP tana rikici a kotu

Uzurin da INEC ta bada shi ne ‘umarnin kotu’, ma’ana ana shari’a a gaban kuliya a kan wanda zai ya wa jam’iyyar PDP takarar kujerar gwamna.

Hakan na zuwa ne bayan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar sun kai kara, kuma suka yi dace aka ruguza zaben da Mr. Oladipupo Adebutu ya samu nasara.

‘Yan Jam’iyyar PDP
Magoya bayan APC a Ogun Hoto: punchng.com
Asali: UGC

APC za ta ci banza?

A gefe guda ita ma jam’iyyar LP mai adawa ba za ta samu damar tsaida wanda zai rike mata tuta a zaben gwamnan jihar Ogun a zabe mai zuwa ba.

Wannan yana nufin Gwamna mai-ci watau Dapo Abiodun zai iya samun abubuwa da sauki idan har aka haramtawa manyan jam’iyyu shiga takara.

Kara karanta wannan

Princewill: Atiku da Peter Obi Za Su Iya Taimakawa Tinubu Ya Ci Zabe a Saukake

Masu shiga takara a 2023

A yau ne hukumar INEC mai zaman kanta, tayi alkawarin za ta fitar da sunayen duk masu neman takarar gwamnoni da kujerun majalisun dokoki.

Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu yace jam’iyyu 18 ne suka tsaida ‘yan takara 837 a zaben gwamnoni da za a gudanar a jihohi 28.

A takarar majalisar dokokin jihohi, ‘yan siyasa 10, 240 suke harin kujeru 993 da ake da su a kasar.

BoT za ta dinke baraka

A daren yau ne aka ji labari 'Yan majalisar BoT na jam’iyyar PDP sun yi zama da ‘Dan takaran Shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar a gidansa.

Yau Adolphus Wabara ya jagoranci zaman farko na majalisarsa da nufin a dinke barakar da ta addabi jam’iyyar PDP da bangaren Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel