Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

  • Yan siyasar Najeriya da jam’iyyunsu sun fara gudanar da yakin neman zabensu na 2023
  • Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya saki wani bidiyonsa da ke nuna lallai yana cikin koshin lafiya
  • Atiku Abubakar na PDP kuma ya nishadantar da yan Najeriya ta hanyar tikar rawar wata waka ta Davido
  • Su dukka biyun sun haddasa cece-kuce a Twitter yayin da wasu da dama suka bayyana cewa duk yaudara ce suke yiwa al’umma

Babban zaben 2023 na kara gabatowa kuma tuni yan takarar shugaban kasa suka fara gudanar da kamfen dinsu yayin da suke kokarin ganin sun karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, bai halarci wasu taruka da aka gudanar a baya-bayan nan ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Tinubu
Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ba a gansa ba yayin da sauran yan takarar shugaban kasa suka hadu don kulla yarjejeniyar zaman lafiya. Maimakon haka, sai ya tura Kashim Shettima wato abokin takararsa domin ya wakilcesa.

Rashin ganin Tinubu a taron ya haddasa cece-kuce harma aka kafa maudu’in #inaTinubu a dandalin Twitter, inda mutane da dama suka bakaci ayi masu bayanin inda ya shiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Domin tabbatarwa masu sukarsa cewa yana cikin koshin lafiya, Tinubu ya saki wani bidiyonsa kan keke yana motsa jiki.

Atiku ya yi rawar wakar Davido

Jim kadan bayan bayyanar bidiyon Tinubu, sai ga wani dan takarar shugaban kasa ya saki nasa bidiyon yana mai nunawa yan Najeriya cewa shi din gwanin iya rawa ne.

Atiku Abubakar mai shekaru 75 ya nuna cewa har yanzu yana da sauran karfinsa a cikin wani dan takaitaccen bidiyon da magoya bayansa suka saki a Twitter.

Kara karanta wannan

Yadda Sowore Ya Kusa Yin Fada da Hamza Al-Mustafa da Kashim Shettima a Taro

Atiku
Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke Hoto: @renoomokri
Asali: Twitter

A bidiyon mai tsawon sakanni 43, an gano Atiku yana rawar wata wakar Davido.

Martanin yan Najeriya game da bidiyoyin Tinubu da Atiku

Ga dukkan alamu dukkanin dattawan biyu na son nunawa yan Najeriya cewa suna da isasshen lafiyan jagorantar kasar.

Jama’a sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyoyin nasu.

Aisha Yesufu @AishaYesufu ta ce daga Tinubu har Atiku suna fafutukar ganin sun burge mutane ne.

Charly Boy Area Fada 1 @AreaFada1 ya yi wata tambaya:

NEFERTITI @firstladyship tayi martani:

“Yayin da Tinubu ya tuka keke don tabbatar da yana raye, Atiku ya yi bidiyon TikTok don tabbatar da shi din matashi ne kuma daya daga cikinmu. Yan Najeriya kada ku tsaya kallon tabbacin rayuwa na wasu shekaru 8. Ba zai yiwu ku dunga kallon kafadunku ba. Ku sani, idan APC ta yi nasara, zasu haramta Twitter gabaki daya.”

Rinu Oduala @SavvyRinu ya yi martani:

“Atiku na rawa a TikTok yayin da Tinubu ke tuka keke. Nayi dariya har na gaji."

Kara karanta wannan

Allah na tuba: Malamin addini ya karbi kudin Tinubu, ya yi nadamar abin da ya aikata

Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila

A gefe guda, mun kawo a baya cewa mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress, Hon Yakubu Murtala Ajaka, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na nan cikin koshin lafiya.

Hon. Ajaka ya kuma bayyana cewa sabanin yadda ake ta yayatawa, babban jigon na jam’iyya mai mulki ba jinya ya tafi yi a Ingila ba, Vanguard ta rahoto.

Ajaka wanda ya ziyarci dan takarar na APC a Landan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel