Rabaran Mbaka Ya Magantu Kan Zaben 2023a, Ya Ce Wasu ’Yan Najeriya Na Bata Lokacinsu Ne Kawai

Rabaran Mbaka Ya Magantu Kan Zaben 2023a, Ya Ce Wasu ’Yan Najeriya Na Bata Lokacinsu Ne Kawai

  • Babban fasto kuma mai yawan jawo cece-kuce a Najeriya ya bayyana irin abubuwan da ya hango gabanin zaben 2023
  • Rabaran Mbaka ya ce, Allah ya sanar dashi wanda zai gaji Buhari, amma ba zai fadi wanene ba saboda dalilai
  • An dakatar da Mbaka a baya can saboda maganganun da yake masu daukar hankali kan shugaban Najeriya

Enugu - Rabaran Eike Mbaka na Adoration Ministry da ke Emene a jihar Enugu ya magantu kan zaben 2023 da ke karatowa a nan gaba kadan, rahoton Tribune Online.

Ya yi magana mai daukar hankali a jiya Lahadi 2 ga watan Oktoba, inda ya bayyana abubuwan da ya hango kan zaben mai zuwa.

Wannan karon ne dai karon farko da Mbaka ya yi magana tun bayan dage takunkumin hana shi wa'azi da kungiyar kiristoci ta yi a baya.

Kara karanta wannan

Kamar almara: Bidiyon yadda budurwa ta taso zakuna a gaba ya girgiza intanet

Fasto Mbaka ya magantu kan makomar Najeriya da shugabanta na gobe
Rabaran Mbaka Ya Magantu Kan Zaben 2023a, Ya Ce Wasu ’Yan Najeriya Na Bata Lokacinsu Ne Kawai | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Mbaka ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutane da dama suna bata lokacinsu ne a zaben 2023 mai zuwa. Allah ya ce kada na fada. Amma kamar yadda abin yake, mutane da dama suna bata lokaci ne."

Ya kuma bayyana cewa, jama'a su zuba ido kawai, komai zai zo karshe.

Ina da mafita ga Najeriya, inji Mbaka

Hakazalika, ya kara da cewa, abu daya ne zai hana shi ba 'yan Najeriya mafita guda mai sauki, rahoton Within Nigeria.

"Idan ba dan gargadin ruhu mai tsarki ba, da zan ba 'yan Najeriya wata mafita mai sauki.
"Amma ku dai jira."

Idan baku manta ba, a baya an dakatar da Rabaran Mbaka daga yin wa'azi saboda fadin maganganu masu tada hankalin jama'a.

A ranar 30 ga watan Satumba ne aka dage wannan dakatarwa, wanda aka kakabawa babban malamin na addinin kirista.

Kara karanta wannan

Ku yi hakuri: Gwamnati ta yi laushi, ta fara lallabi da rokon ASUU ta janye yaji

Bola Tinubu Ne Ya Fi Cancantar Zama Shugaban Kasa, Inji Uba Sani

A wani labarin, dan takarar gwamna a jihar Kaduna a jam'iyyar APC, Uba Sani ya ce dan takararsu na APC da ke neman gaje kujerar Buhari ne mafi cancantan zama shugaban kasa a zaben 2023.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton cewa, jam'iyyar APC ta tsayar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasan a zabe mai zuwa nan da badi.

Uba sani, wanda sanata ne mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya ce Tinubu ya yi amfani da karfi da dukiyarsa wajen ciyar da dimkoradiyya gaba a kasar nan yayin da wasu 'yan takarar kuma tubabbun 'yan mulkin soja ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel