Bidiyon Budurwa Na Tafiya da Zakuna Kamar Karnuka Ta Jawo Cece-Kuce a Intanet

Bidiyon Budurwa Na Tafiya da Zakuna Kamar Karnuka Ta Jawo Cece-Kuce a Intanet

  • Wata mata ta yada bidiyon lokacin da take tafiya tare da wasu zakuna guda uku a gabanta ba tare da tsoro ko firgita ba
  • Matar da ta ta tasa zakunan a gaba lokacin da take tare da wani kwararren mai gadin gidan dabbobi ta ce wannan lamari ya zame mata tarihin da ba za ta taba mancewa ba
  • Mutane da dama da suka ga bidiyon a TikTok sun bayyana kaduwarsu da ganin wannan abu mai ban mamaki

Wata budurwa a TikTok mai suna @ituhadebetsubane ta yada wani bidiyonta a kafar sada zumunta na yadda ta kasance tare da wasu zakuna a gidan ajiye dabbobi.

A bidiyon da miliyoyin jama'a suka gani a kafar, an ga budurwar na rike da sanda yayin da ta saka wasu manyan zakuna uku a gaba.

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

Kasancewar tana rike da sanda, an ga tana tafiya a bayansu, su kuwa suna gaba kamar dai mai kare da karnukansa.

Bidiyon wata budurwa ya ba da mamaki
Bidiyon budurwar da ka tafiya da zakuna kamar karnuka ta jawo cece-kuce a intanet | Hoto: TikTok/@ituhadebetsubane
Asali: UGC

A bidiyon, ta ce wannan ganawa tata da zakuna lamari ne da ba zata taba mantawa dashi ba a rayuwa, kuma mutane da dama sun yi martani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa a kafar sada zumunta

Tammy McCartean yace:

"Kamar dai wadannan zakunan basu ga abincin ranansu a bayansu bane"

SM yace:

"Bidiyo mafi kyau da na taba gani kenan. Kamar dai zakunan na kare kyakkyawar budurwar ce."

Nicole yace:

"Gaskiya ne sarauniya!!! Ki rike mana shi da kyau a Afrika ga duk wata sarauniya a Amurka da fadin duniya."

Priscilla Rodriguez tace:

"Suna da jiji da kai....jiji da kai... dabbobin da Allah ya halitta"

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Leigha yace:

"Jami'an kariya mafi kwarewa kenan."

Matashi Mai Shekaru 38 Ya Koma Makarantar Firamare Yayin da Matarsa Ta Guje Shi

A wani labarin, wani magidanci dan shekara 38 ya bayyana komawa karatu saboda ya nemi ilimin da zai zama wani abu nan gaba.

Matashin mai suna John ya koma makarantar firamare domin ya samu nagartaccen ilimi duk kuwa da yawan shekarunsa.

John dai na da kyakkyawar mata da 'ya'ya biyu, amma da zama ya yi tsami, matar ta guje shi ta bi wani mutum daban, inda ta kira John lusari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel