Ku Janye Yajin Aikin Nan Don ’Ya’yanmu Mu, Kakakin Majalisa Ya Roki ASUU

Ku Janye Yajin Aikin Nan Don ’Ya’yanmu Mu, Kakakin Majalisa Ya Roki ASUU

  • Yayin da yajin aikin ASUU ke kara kamari, gwamnatin Najeriya na ta tunanin hanyoyin da za a kawo mafita
  • Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya magantu da ASUU, ya roki su gaggauta janye yajin aiki
  • Ministan kwadago ya ce ba zai yiwu gwamnatin Buhari ta ba ASUU abin da babu shi ba, don haka su yi hakuri

FTC, Abuja Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai a Najeriya ya yi kira ga kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU da su duba tare da janye yajin aiki saboda biyan muradan dalibai a kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin dagawa da ASUU, ministan kwadago Chris Ngige da mukaddashin akanta janar na kasa Okolieaboh Sylva a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

2023: Peter Obi Ya Bayyana Shirin Da Ya Yi Wa Ƴan Bindiga, Da Masu Neman Ɓallewa Daga Ƙasa Idan An Zaɓe Shi

Kakakin na majalisa ya ce an biya bukatar majalisar a yanzu kam, TheCable ta ruwaito.

Kakakin majalisa ya roki ASUU su janye yajin aiki
Ku Janye Yajin Aikin Nan Don Biyan Mudain ’Ya’yanmu Mu, Kakakin Majalisa Ya Roki ASUU | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba zai yiwu a ce kowa ya yi kuskure ba. Muna tafiya kan abin da muka ce a zamanmu na karshe, don Allah saboda muradin 'ya'yanmu, muna rokonku ba wai don umarnin kotu ba."

Gbajabiamila ya ce ana yin mai yiwuwa domin ganin an tabbatar da warware batutuwan da suka shafi tsarin biyan albashin UTAS da ASUU ta ke son amfani dashi.

Ya kuma ce ya fahimci ba suna fushi ne don karan kansu ba, suna yi ne domin kawo mafita ga 'yan baya.

Ku karbi tsarin albashin bai daya na IPPIS

Shi kuwa da yake magana, mukaddashin akanta janar na kasa ya roki ASUU da su runguma tare da amince da tsarin albashin gwamnati na IPPIS.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Dan takarar shugaban kasa ya fadi abu daya zai yi ya magance yajin ASUU

Ya kuma bayyana cewa, idan ma akwai wata bukata ta kudaden alawus-alawus, ofishinsa zai tabbatar da ba ASUU wadannan bukatu.

Ya shaidawa ASUU cewa:

"Ya kamata mu zauna mu san wadannan abubuwan kuma mu magance a cikin IPPIS. Za mu gyara duk inda muka yi kuskure yanzu."
"Idan muka amince da batun ASUU, zai ba da kofa ga sauran ma'aikata su ce a basu damar kawo hanyar albashinsu, sojoji da ma'aikatan lafiya duk a kan IPPIS suke, ya kamata ASUU ta zauna damu da ga irin ci gaban da muka samar."

Ya kuma ce babu wata matsala idan ASUU ta amince da karbar tsarin biyan albashin na IPPIS.

Gwamnati ba za ta ba ASUU babu ba, inji Ngige

A nasa jawabin, ministan kwadago Ngige ya ce gwamnatin tarayya ba za ta ba ASUU abin da bata dashi ba.

Ministan ya ce, tun farko ya zo tabbatar da amfani da UTAS da sauran hanyoyin biyan albashi guda biyu da ASUU ta kawo.

Kara karanta wannan

Zan saurari su Nnamdi Kanu, amma babu ruwana da 'yan bindiga, inji Peter Obi

Sai dai, a cewar Ngige, dukkan hanyoyin da ASUU ta kawo sun gaza tsallake tantancewar da aka gwada su a kai.

Da yake martani, shugaban ASUU, Emmaneul Osodeke ya ce, yana matukar ciwo ganin yadda 'yan Najeriya suka gaza fahimtar yadda tsarin jami'o'i ke tafiya.

Bankin CBN Zai Fara Cire Kudi Daga Asusun ’Yan Najeriyan da Suka Ci Bashin Gwamnati

A wani labarin, babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara zare kudade daga asusun bankin gwamnatin jihohi da wasu 'yan Najeriya domin warware bashin da ake binsu.

Daraktan raya fannin kudi na CBN, Yusuf Yila ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba 30 ga watan Satumba, The Cable ta ruwaito.

Yila ya ce babban bankin ya shirya karbo kudade daga gwamnati jihohi da manoma ne da suka ci gajiyar kowane daga shirye-shiryen rance na gwamnati tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel