Zaben 2023: Tinubu Da APC Sun Yi Babban Rashi A Yayin Da Jigon Jam'iyyar Mai Mulki Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

Zaben 2023: Tinubu Da APC Sun Yi Babban Rashi A Yayin Da Jigon Jam'iyyar Mai Mulki Ya Sauya Sheka Zuwa PDP

  • Ana rikici a sansanin manyan jam'iyyun siyasan Najeriya wato jam'iyyar APC da PDP
  • Rikicin ya janyo sauya sheka tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, daga PDP zuwa APC da kuma kishiyan haka
  • Watanni kadan kafin babban zaben shekarar 2023, jigon jam'iyyar APC, Honarabul Ibinabo Dawari ya fita daga APC ya koma PDP a Rivers

Jihar Rivers - A yayin da ake tsakiyar rikici kan kwamitin yakin neman zabe na Asiwaju Bola Tinubu, wani jigo na jam'iyyar mai mulki a kasa a jihar Rivers ya yanke shawarar barin jam'iyyar.

Jigon na APC kuma tsohon ciyaman na rikon kwarya a karamar hukumar Asari-Toru, Hon Ibinabo Dawari ya fita daga jam'iyyar APC ya koma PDP.

Ibinabo Dawari
2023: Tinubu Da APC Sun Yi Babban Rashi A Yayin Da Jigon Jam'iyyar Mai Mulki Ya Sauya Sheka Zuwa PDP. Hoto: Rivers Mirror.
Asali: Facebook

Honarabul Ibinabo ya bada dalili

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

Hon. Dawari, wanda tsohon na hannun daman shugaban karamar hukuma, Hon. Ojukaye Amachree, ya ce ya sauya shekar ne don yana son yi wa PDP aiki babu kama hannun yaro a jihar, Rivers Mirror ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar, don haka ya ce zai yi aiki don ganin Sir SIM Fubara, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP da sauran yan takara a kananan hukumomi sun yi nasara.

An yi wa Hon Ibinabo Dawari tarba ta musamman zuwa PDP

Da ya ke tarbar tsohon shugaban na CTC a sakatariya da ke Buguma City, Hon. Onengiyeofori George ya bashi tabbacin ba za a nuna banbanci tsakaninsa da sauran yan jam'iyyar ba kuma ya jinjinawa jarumtarsa na barin jam'iyyar hamayyar a Jihar Rivers.

Hon. George ya ce ana fatan PDP za ta samu gaggarumin nasara a zabukan gwamna, sanatoci da sauransu duba da irin ayyuka da romon demokradiyya da jam'iyyar ta shayar yan jihar.

Kara karanta wannan

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel