Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

Babu Banbanci Tsakanin Obi, Atiku Da Tinubu, In Ji Kachikwu, Dan Takarar Shugaban Kasa Na ADC

  • Mr Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya ce jirgi daya ya kwaso Obi, Atiku da Tinubu
  • Kachikwu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a gidan talabijin na Channels
  • Dan takarar shugaban kasar na ADC ya ce yan Najeriya sun gaji tsaffin yan siyasa domin an basu dama a baya ba su tabuka wani abin azo a gani ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Democratic Congress, ADC, Mr Dumebi Kachikwu ya ce babu banbanci tsakanin dan takarar APC, Bola Tinubu, na PDP Atiku Abubakar da dan takarar Labour Party, Peter Obi, Daily Trust ta rahoto.

Kachikwu ya bayyana hakan ne a shirin Polics Today na gidan talabijin na Channels TV, yana mai cewa yana cikin sabbin jini da yan Najeriya ke bukata domin canja gwamnati.

Kara karanta wannan

2023: Bayanai Sun Fito, Atiku Zai Gana Da Wasu Ƙusoshin Jam'iyyar PDP Na Kudu Maso Gabas

Kachikwu
Obi bashi da banbanci da Tinubu, Atiku - Kachikwu, dan takarar shugaban kasa na ADC. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Dukkansu ukun tsaffin yan siyasa ne kuma ba su da wani sabon abu da za su kawo. Babu banbanci tsakanin Peter Obi, Atiku da Asiwaju.
"Babu dalilin da zai sa mu fito tare muna neman mulki. Ban shiga takarar don na matsu da samun mulki ba. Na shiga takarar ne domin ina ganin kasa ta tana bukatar canji matuka.
"Yan Najeriya na bukatar sabon zubi. Tsawon lokaci, tsiraru masu karfin fada a ji ke juya kasar, a wannan zaben, masu rinjaye marasa hayaniya sun shirya kuma za su kwace kasarsu."

Babban Jam'iyya A Najeriya Ta Dakatar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta

A wani rahoton, Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC ta dakatar da Mr Dumebi Kachikwu, dan takarar shugaban kasarta, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Hakan na zuwa ne awanni bayan da Mr Kachikwu ya goyi bayan kiran da ciyamomin jam'iyyar suka yi na cewa Ralph Nwosu, shugaban jam'iyyar na kasa ya yi murabus bayan shekaru 17 a ofis.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar, Mr Babajide Ajadi, mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, ya ce kwamitin koli na jam'iyyar wato NEC ce ta dauki matakin a taron da ta yi ranar Juma'a.

Ajabi ya ce tun bayan da Kachikwu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, ya gaza fitar da tsarin yadda zai gudanar da kamfen dinsa da za a fara nan bada dadewa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel