Rigima ta kunno APC, Gwamnonin Jam’iyya na Shirin Yi wa Bola Tinubu Zagon kasa

Rigima ta kunno APC, Gwamnonin Jam’iyya na Shirin Yi wa Bola Tinubu Zagon kasa

  • An ba kowane Gwamna dama ya kawo sunayen wadanda za a sa a kwamitin takarar Bola Tinubu
  • Ko da sunaye suka fito, sai ga wasu Gwamnonin APC suna kukan ‘Dan takaran ya yi watsi da maganarsu
  • Sabanin ya yi kamari da an samu Gwamnonin da ke yi wa Tinubu barazanar kin goyon bayan takararsa

Abuja - Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi barazanar kawowa takarar Asiwaju Bola Tinubu cikas a jihohinsu a 2023.

Wani rahoto na musamman da muka samu daga Premium Times a ranar Litinin, ya bayyana cewa ‘yan kungiyar PGF suna jin haushin Bola Tinubu.

Gwamnonin APC sun fusata ne a kan yadda jam’iyya da ‘dan takararta suka yi watsi da sunayen da suka bada na wadanda za a sa a kwamitin kamfe.

Kara karanta wannan

Kakakin Kamfen Ɗin Atiku Ya Fallasa Dalilin Da Yasa Osinbajo Da SGF Suka Ƙi Shiga Kwamitin Kamfen Ɗin Tinubu

Gwamnonin jihohi sun samu damar aiko da sunayen ‘ya ‘yan APC biyar da za su shiga cikin kwamitin jam’iyya na yakin neman zaben shugaban kasa.

Magana ta canza daga baya

Abin da ya ba gwamnonin na APC mamaki shi ne, da aka fitar da jerin sunayen ‘yan kwamitin kamfe, sai suka ga an yi watsi da sunayen da suka gabatar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu sun yi wannan ne ba tare da sanin gwamnonin ba. Wannan ya jawo aka yi ta kai wa APC da PGF korafi.

To, ayi dai mu gani - Gwamnoni

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Ribas yace ba zai ba Tinubu gudumuwa wajen kamfe ba tun da an fi shi sanin jiharsa.

Shi ma Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, yace sunaye biyar ya bada, amma sunan mutum daya ya gani cikin mutane bakwai daga jiharsa.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan VP Yemi Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba, Jam'iyyar APC

Abin ya kai su Rotimi Akeredelu suna kai wa jam’iyya kukan an yi watsi da sunayen wadanda gwamnoni suka bada, duk da su suka san ‘yan siyasan ainihi.

Asiwaju Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu mai takara a APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Baraka a Arewa

Gwamnonin Arewa maso yamma su na zargin Tinubu bai tafiya da su a takararsa. Sai da sunan ‘yan kamfe ya fito sai abin da suke zargi ya gaskata.

Wata majiya tace gwamnonin wannan yanki suna ‘dan takaran ya raina su, kuma idan ya yi sake, za su iya hana shi lashe zabe a Arewa maso yamma.

Ka ji da naka - Atiku ga Tinubu

A makon jiya, kun ji labarin yadda Hadimin Atiku Abubakar ya dura kan Bola Tinubu mai neman mulki a APC, a dalilin kalaman da ya yi kan rikicin PDP.

Paul Ibe ya fadawa Tinubu ya daina yi wa PDP katsalandan saboda wani sabani tsakanin Nyesom Wike da ‘dan takaranta, wanda aka saba a siyasa.

Kara karanta wannan

Akwai Sanatan PDP, amma babu Yemi Osinbajo a Kwamitin yakin zaben Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel