Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba

Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba

  • Jam'iyyar APC ta yi fashin baki kan rashin sunan mataimakin shugaban kasa a kwamitin kamfe
  • Daya daga cikin masu magana da yawun kamfen yace shugaba Buhari da kansa yace kada a sa Osinbajo
  • An fara rade-radin cewa an yi watsi da Osinbajo ne saboda fit-na-fito da yayi da Tinubu a zaben fidda gwani

Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta yi fashin baki kan dalilin da yasa ba'a sa sunan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Ostinbajo, cikin kwamitin yakin neman zabenta ba.

Jam'iyyar APC ta saki jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zabenta a daren Asabar, 24 ga watan Satumba 2023.

Kwamitin mai adadin mambobi 442 ya hada da shugabannin jam'iyyar, gwamnoni, tsaffin gwamnoni, har da shugaban kasa.

Abin mamaki shine akwai sunan kusan kowa a ciki amma an nemi na Osinbajo an rasa.

Kara karanta wannan

Akwai Sanatan PDP, amma babu Yemi Osinbajo a Kwamitin yakin zaben Tinubu

Wasu sun fara jawabin cewa an yi watsi da Osinbajo ne saboda fit-na-fito da yayi da Tinubu a zaben fidda gwani.

Tinubu/Osi
Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba Hoto: APCconvention
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma mai magana da yawun kwamitin Festus Keyamo ya bayyana cewa shugaba Buhari da kansa yace kada a sa sunan Yemi Osinbajo.

Keyamo ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Asabar mai take 'Rashin sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kwamitin kamfe ba abin damuwa bane'.

Yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya yi umurnin kada a sa sunan Shugaban kasa da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a kwamitin kamfe saboda su mayar da hankali kan harkar mulki."
"A matsayinmu na gwamnati mai hankali, ba zai yiwu dukkan rassan gwamnati su ajiye ayyukansu ba don kamfe."

Sunan Sanata PDP, Chimaroke Nnamani Ya Fito Cikin Kwamitin Kamfen APC

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP kuma Sanata mai wakiltar mazabar Enugu Ta Gabas, Chimaroke Nnamani ya samu shiga cikin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress, APC,.

Jam'iyyar APC ta saki sunayen mutanen da zasu taka rawar gani wani ganin tayi nasara a zaben 2023.

Wani suna guda daya da akayi mamakin gani shine na tsohon gwamnan jihar Enugu, Chimaroke Nnamani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel