2023: Cikakkun Sunayen Yan Kannywood Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

2023: Cikakkun Sunayen Yan Kannywood Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta fitar da jerin sunayen shugabanni da mambobin kungiyar kamfen din dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Wasu manyan jaruman kannywood sun samu shiga wannan kwamitin karkashin rukunin masu nishadantarwa
  • Shugaban hukumar tace fina-finai na Kano, Afakalla, Nuhu Abdullahi, Rarara da Sani Idris Moda sun shiga jerin

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta nada wasu shahararrun yan masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood a matsayin mambobi a kungiyar kamfen din shugaban kasa na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ana sanya ran wadannan mutane da aka nada su jagoranci nemawa dan takarar goyon baya gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.

Tinubu, Nuhu da Afakallah
2023: Cikakkun Sunayen Yan Kannywood Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu Hoto: officialasiwajubat, ismail_naabba_afakallah, nuhuabdullahi
Asali: Instagram

An nada Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma'ila Na'abba Afakalla a matsayin mataimakin daraktan masu wasanni a kwamitin kuma zai jagorancin yankin arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan VP Yemi Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba, Jam'iyyar APC

Hakazalika shahararren mawakin siyasa, Daudu Kahutu Rarara ya samu shiga jerin a matsayin jami’in kula da harkokin kwamitin na yan wasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai fitaccen dan wasa Nuhu Abdullahi a matsayin mataimakin mai kula da jin dadin kwamitin yan wasan.

Sani Idris Moda ma ya samu shiga kwamitin kaamfen din tsohon gwamnan na jihar Lagas a matsayin dattijan kungiya.

Gaba daya dai jimilar yan Kannywood hudu ne suka samu shiga wannan kwamiti na babban jam’iyya mai mulki a kasar.

Ga cikakken sunayen a kasa:

Sunayen yan kamfen din Tinubu
Cikakkun Sunayen Yan Kannywood Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu Hoto: @APCPresCC2022
Asali: Twitter

Dalilin Da Yasa Bamu Sa Sunan Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo A Kwamitin Kamfen Ba

A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ta yi fashin baki kan dalilin da yasa ba'a sa sunan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Ostinbajo, cikin kwamitin yakin neman zabenta ba.

Kara karanta wannan

Akwai Sanatan PDP, amma babu Yemi Osinbajo a Kwamitin yakin zaben Tinubu

Jam'iyyar APC ta saki jerin sunayen mambobin kwamitin yakin neman zabenta a daren Asabar, 24 ga watan Satumba 2023.

Kwamitin mai adadin mambobi 442 ya hada da shugabannin jam'iyyar, gwamnoni, tsaffin gwamnoni, har da shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel