Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023

Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023

  • Rikicin jam'iyyar APC kan tsayar da takara Musulmi da Musulmi ya buɗe sabon shafi yayin da wasu suka fara shirin yaƙi
  • Tsohon SGF, Babachir Lawal, yace zasu hana idonsu bacci don tabbatar da shirin APC bai kai ga nasara ba a zaɓen 2023
  • Yace zasu haɗa kai da wata jam'iyya mai ƙarfi domin ba zasu yarda kuri'un kiristocin arewa su tafi a banza ba

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Babachir Lawal, yace jam'iyyar APC ta tsayar da tikiti Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban kasa na 2023 ba don komai ba sai don tarwatsa arewacin Najeriya.

Lawal ya yi wannan furucin ne yayin da yake martani kan jerin sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya na ƙarshe da hukumar zaɓe INEC ta fitar.

Babachir Lawal Yana Jawabi.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023 Hoto: Babachir Lawal
Asali: Facebook

Da yake tsokaci game da lamarin a wata hira da Arise TV ranar Laraba, Lawal yace Kiristocin arewa 'yan siyasa sun shirya ganin bayan takarar mabiya addini ɗaya da APC ta tsiro da shi.

Kara karanta wannan

Akwai Wasu Mutane Dake Yi Wa Shugaba Buhari Zagon Ƙasa, Gwamna Yahaya Bello

Daily Trust tace a kalamansa, Babachir Lawal yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Samar da tikitin Muslim-Muslim ko mu ce mabiya addini ɗaya wani sheɗanin shiri ne da zai raba kawuna a arewa. Muna kokari a matsayin jagororin al'umma mu rayu a matsayin yan uwa amma an zo mana da wata tsirfa."
"Duk mai ƙaunar haɗin kai a kasar nan musamman a arewa inda aka zalunce mu da wannan tikitin ba zai kai ga nasara ba, kuma zamu tabbatar mun ga bayan shi ta yadda babu wani mai hankali da zai ƙara tunanin makamancin haka a gaba."
"Saboda mun gama shiri sannan zamu ga bayansa (Takara Musulmi da Musulmi), mutanen mu sun taru wuri guda kuma sun shirya wa zaɓe."

Jiga-Jigan APC zasu yaƙi Tinubu

Bugu da ƙari, tsohon SGF ya ƙara da cewa shi da tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, zasu jagoranci tawagar kiristocin arewa wajen kayar da APC.

Kara karanta wannan

INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa da Mataimakansu Na Karshe Gabanin 2023

"Ni da Yakubu Dogara ba mu kaɗai lamarin ya sosa wa zuciya ba, amma mune zamu jagoranci kungiyoyin Kiristoci 40 dake siyasa a arewa, tuni muka fara aiki saboda mun yi zargin haka zaka faru idan ɗan takara musulmi ya fito daga kudu."
"Yayin da muka yi shirin ganin bayan takarar masu addinin ɗaya na APC, Zamu haɗa kai da jam'iyyar siyasa mai karfin cin nasara. Dabarar mu shi ne bamu son asarar kuri'u saboda muna son koya wa APC darasi."

A wani labarin kuma shugaban BoT-PDP yace duk da komai ya lalace amma ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen warware sabanin Atiku da Wike

Shugaban BoT na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Sanata Wabara, ya kai ziyarar neman sulhu ga gwamna jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Tsohon shugaban majalisar dattawa yace komai ya dagule a PDP amma nan ba da jimawa ba zasu shawo kan komai.

Kara karanta wannan

ASUU: Kar Ku Kai Matasa Bango, Ba Zamu Iya Shawo Kansu Ba Idan Suka Tunzura, Wani Sarki Ya Gargaɗi Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel