Lagon Atiku a Kebbi Ya Yi Sako-Sako, Jiga-Jigan PDP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Lagon Atiku a Kebbi Ya Yi Sako-Sako, Jiga-Jigan PDP da Yawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Rahoton da muke samu daga jihar Kebbi na bayyana cewa, wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC
  • Jam'iyyar APC a jihar ta karbe su, ta kuma ba su damar fadin abubuwan da ya ja suka bar jam'iyyar PDP ta adawa
  • Ana ci gaba da bikin sauya sheka yayin da ake ci gaba da jiran zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba

Jihar Kebbi - Jam'iyyar APC a jihar Kebbi ya karbi wasu jiga-jigan siyasan da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP, PM News ta ruwaito.

Daya daga jiga-jigan da suka sauya sheka akwai tsohon babban oditan PDP, Alhaji Rabi'u Sa'idu, tsohon sakateren kwamitin riko na PDP Alhaji Sirajo Ibrahim da wasu manyan mambobin PDP 15 daga unguwar Bubuce a karamar hukumar Augie ta jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya je daurin auren dan gwamnan Gombe, ya roki Gombawa alfarma daya

Jiga-jigan PDP da dama a jihar Kebbi sun koma APC
Lagon Atiku a Kebbi ya yi sako-sako, jiga-jigan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Sauran sun hada da Umaru Wakkala, mataimakin shugaban PDP na Bubuce; Salihu Shayi, shugaba matasan yankin; Alhaji Idi Babuce, ma'ajin jam'iyya da kuma Hamza Akilu, oditan jam'iyya.

Dalilin komarsu APC

Jim kadan bayan bayyana shiga APC, tsohon babban oditan, ya yaba da irin ayyukan da gwamna Atiku Bagudu ke gudanarwa a jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma ce, ya fice daga PDP ne saboda rashin adalci da kuma tauye musu hakki da ake yawan yi a jam'iyyar, rahoton Punch.

Sa'idu ya kuma yabawa Magajin Rafin Kabı da Alhaji Bello Dantani a kokarinsu na ganin sun daura shi a turbar shiga jam'iyyar APC tare da mabiyansa.

Shi kuwa Augie cewa ta yi:

"Na yaba da aikin titin da aka yi a karamar hukumar Augie a karkashin mulkin sanata Abubakar Atiku Bagudu.
"Wannan hanyan da aka yi a karkashin mulkin sanata Abubakar Atiku Bagudu na daya daga cikin masu muhimmanci."

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Hadimin Gwamnan Kaduna da Mambobin APC Sama da 13,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban APC na karamar hukumar, Alhaji Bashir Isah-Mera; Lawal Muhammad-Yola, shugaban karamar hukumar Augie; Alhaji Haruna Maitandu, shugaban hukumar jin dadin alhazzai, da tsohon daraktan ma'aikatar kwadago, Alhaji Bello Dantani.

Ku Yi Watsi da Tinubu, Atiku da Obi, Shawarin Kwankwaso Ga ’Yan Najeriya

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba 'yan Najeriya shawari kyauta, ya su kiyayi kansu su yi watsi da 'yan takarar shugaban kasa a APC, PDP da LP.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi Bola Ahmad Tinubu, Atiku Abubakar ko Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa, Premium Times ta ruwaito.

A fahimtar Kwankwaso, ya kamata 'yan Najeriya su nisance 'yan takarar saboda basu da wani abin a zo a gani da za su iya ba kasar bayan an zabe su.

Kara karanta wannan

Yan Jam'iyyar PDP 7000 Sun Sauya Sheka APC A Jihar Sakkwato

Asali: Legit.ng

Online view pixel